Waiwaye: Shin a shekaru 18 me dimokuradiyya ta tsinananwa talaka?

Waiwaye: Shin a shekaru 18 me dimokuradiyya ta tsinananwa talaka?

- Mulkin soja dai ya gushe shekaru 18 da suka wuce, shin menene ribar da ake ta cewa talakawa na samu wadda tafi ta mulkin soja? An sami karuwar arziki? Talaka na darawa? Shin 'yan siyasa yaudarar jama'a kawai suke yi?

- Waiwayen NAIJ.com za ta duba ina aka kwana kuma ina ake a jiya, kuma ya gobe ke iya kasancewa?

A shekarun da aka kwashe ana mulkin soja a Najeriya, babu wani muhimminc ci gaba da jama'a ke iya nunawa balle ba damar fada a ji su. Shi dai mulkin soja, mulki ne na kama karya, domin ba zabo su akayi ba, karfin bidiga ne ya dora su, don haka ba'a ma rutsa su da tuhumar ina kudin talakawa, sai su rufe mutum ko su harbe.

Ana dai iya cewa, tun da dimokuradiyya tazo, an sami ci gaba kamar su, ingantar wutar lantarki, samar da wayoyin salula, karuwar ayyukan yi a jihohi da tarayya, habakar noma da zuba jari daga kasashen waje, da ma cire wa kasar takunkumai na karya tattali da a da aka kakaba mata.

KU KARANTA KUMA: Najeriya za ta halaka idan Buhari bai ci zabe karo na biyu ba – hukumar shirya gangamin zabe

Waiwaye: Shin a shekaru 18 me dimokuradiyya ta tsinananwa talaka?

Waiwaye: Shin a shekaru 18 me dimokuradiyya ta tsinananwa talaka?

Amma a harkar tsaro ci baya ne aka samu, domin kowa na iya baje kolinsa da sunan 'yancin fadin albarkacin baki, yaki da ta'addanci ya zama kafa da 'yan siyasa da sojoji ke sace kudaden jama'a.

KU KARANTA KUMA: YANZU YANZU: Aisha Buhari ta tafi birnin Landan don ganin mijinta

A dai yanzu akwai abubuwa sosai da koda ba'a yaba ba, baza a fallasa ba. Ana dai ganin lallai in an kwatanta harkokin biyu, za'a iya cewa, kwai a baka, yafi kaza a akurki.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel