Madallah! An gudanar da addu'o'i na musamman ga Buhari a wannan jihar ta Arewa

Madallah! An gudanar da addu'o'i na musamman ga Buhari a wannan jihar ta Arewa

- A jihar Taraba an gudanar da addu’oi na masamman na zaman lafiya a Najeriya da kuma shugaba Muhammadu Buhari, da fatan Allah ya bashi lafiya.

- Yayin taron addu’ar da Malamai da dama suka jagoranta an karanto Al-Quran, da addu’o’i da kuma yin tawassuli da darajan wannan watan.

Ustaz Shuaibu Muhammad na kungiyar Izala wanda ya kasance daya daga cikin jagororin i wannan addu’ar, yace yiwa Najeriya da shugabanta addu’a ya zama wajibi domin ci gaban kasar da kuma samun walwala cikin wadata ga ‘yan kasar.

Alh. Adamu Tibanson Garkuwan Dakka ya kwatanta shugaba Buhari da jagoran canji da ya cancanci addu’a a wannan lokaci.

NAIJ.com ta samu labarin cewa yayin da wasu ke addu’o’i, wasu ko na ganin ana neman wuce makadi da rawa game da batun rashin lafiyar shugaban kasan ta hanyar neman siyasantar da batun.

Madallah! An gudanar da addu'o'i na musamman ga Buhari a wannan jihar ta Arewa

Madallah! An gudanar da addu'o'i na musamman ga Buhari a wannan jihar ta Arewa

Muhammad Ibrahim wani dan jarida a Najeriya na ganin wasu na neman bangarartar da batun rashin lafiyar shugaba Buhari abinda yace hakan bai dace ba.

Muhammad Ibrahim wanda ya caccaki malaman addini dake zakewa, yace kamata yayi a bar shugaba Buhari ya cigaba da jinya maimakon cewa dole ya cigaba da mulki.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel