Kasar Saudiyya zata kara harajin kudi ga masu saye da kuma shan taba sigari

Kasar Saudiyya zata kara harajin kudi ga masu saye da kuma shan taba sigari

A wani yunkuri na kara samun kudin shiga tare da rage yawan masu zukar taba Sigari a kasar Sa'udiyya mahukuntan kasar sun amince da wata sabuwar dokar karin haraji ga masu saye da sayar da taba Sigari daga ranar 10 ga watan Yulin wannan shekarar.

Shugaban sashin Zakka da karbar harajin kasar ta Khalid Khuraish shine ya bayyana haka a wani gidan talabijin din kasar mai suna Al-Arabiyya, inda ya ce harajin ba a kan masu shan taba sigari kadai zai tsaya ba, har da masu amfani da kayan kara kuzari dangin lemon kwalba da dai sauransu.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Khalid ya ci gaba da cewa, harajin ya tashi daga Riyal biliyan 8 zuwa Riyal biliyan 10 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.1 zuwa dala biliyan 2.7 a shekara, wanda ya yi kwatankwacin karin kaso 50 cikin dari na harajin da ake biya a baya.

Kasar Saudiyya zata kara harajin kudi ga masu saye da kuma shan taba sigari

Kasar Saudiyya zata kara harajin kudi ga masu saye da kuma shan taba sigari

Canji a haraji yana taka muhimmiyar rawa a samun kudin shigar kasar Sa'udiyya, domin a shekarar da ta gabata mun yi kasafin kudin da ya kai darajar Riyal biliyan 297, kuma haraji shine kaso mai tsoka wajen samar da kudin kasafin. Sannan muna so mu cimma kasafin kudin shekarar 2020 duk da harajin, in ji Khalid.

Yanzu haka kasashe 6 na yankin Golf su ma sun aminta da dokar karawa taba sigari haraji, domin samun kudin shiga.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan
NAIJ.com
Mailfire view pixel