An bawa mulkin Buhari karamin maki a cikarsa shekara 2

An bawa mulkin Buhari karamin maki a cikarsa shekara 2

- Wani jigo a jam'iyyar adawa ta PDP ya ce gurguwar tafiya ake a gwamnatin APC

- An sami shekaru biyu kenan ana mulkin APC

Masu karfin fada aji a jam'iyyar PDP na cewa babu wani katabus da mulkin APC ya yi, kuma gwamnatin Buhari bata ko yi wani abun kuzo ku gani ba a tafiyar tasu tun 2015.

Mr. Oguntuase yace sai ma karuwar talauci da kaka-nikayi da gwamnatin APC da ta jefa talakawa ciki.

Ya kara da cewa, tsantsar rashin adalci ne ace ana yaki da cin hanci da rashawa bayan kuma mutanen tsohuwar jam'iyyarsu ta PDP ce kawai ke shan wahalar kamen da kullewa.

KU KARANTA KUMA: Mu taru mu ceci tattalin arzikin kasar mu - Inji Bukola Saraki

An bawa mulkin Buhari karamin maki a cikarsa shekara 2

An bawa mulkin Buhari karamin maki a cikarsa shekara 2

Mr. Oguntuase yace zuki ta malle ce kawai wai APC tace tayi wata rawar gani a shekaru biyu da tayi a kan mulki kasa da jihohi. Yace tun irin zabe na adalci na tsohon shugaba Goddluck Jonathan, babu wani zaben adalci da aka kara yi.

Ana dai bikin cikar Najeriya shekara 18 a kan turbar dimokuradiyya, a yau dinnan litinin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel