Gidan sama hawa 3 ya ruguje a jihar Legas, rayuwaka da dama sun salwanta

Gidan sama hawa 3 ya ruguje a jihar Legas, rayuwaka da dama sun salwanta

- Bene hawa uku ya ruguzo a Legas, jama da dama sun rasu

- Hukumar bada agajin gaggawa na cigaba da taimaka wajen aikin ceto

Ana fargabar mutuwar jama’a da dama bayan wani katafaren gidan sama mai hawa uku ya ruguzo a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wannan gida na lamba ta 24 kan titin Daddy Alaja a unguwar Apongbon na jihar Legas, kuma har zuwa lokacin hada wannan labara, majiyar NAIJ.com bata gani musabbabin abin da yayi sanadiyyar ruguzowar gidan ba.

KU KARANTA: Yan Najeriya sun gamsu da kamun ludayin gwamnatin mu – Osinbajo

Sai dai an ruwaito ana nan ana gudanar da aikin ceton jama’a, amma duk da haka, jami’an hukumar bada agajin gaggawa na shan wahalar gudanar da ceton.

Gidan sama hawa 3 ya ruguje a jihar Legas, rayuwaka da dama sun salwanta

Gidan sama hawa 3 daya ruguje

Wasu majiyan gani da ido sun bayyana cewa da alamu mutane dayawa sun mutu ciki har da kananan yara sakamakon gidan na haya ne, amma kuma sun tabbatar da cewar an ceto wasu mutane biyu mace da namiji, kuma an garzaya dasu Asibiti.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Biafra: Osinbajo yayi bayani

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel