Mu taru mu ceci tattalin arzikin kasar mu - Inji Bukola Saraki

Mu taru mu ceci tattalin arzikin kasar mu - Inji Bukola Saraki

- Mu taru mu ceci dimokuradiyya da tattalin arzikinmu

- Sanarwar tunawa da ranar dimokracy ta Najeriya da ya fitar, na kira a hada kai a ciyar da kasa gaba

- Ana bikin zagayowar ranar dimokuradiyya

A sanarwar da ta mai taya shugaban Majalisa harka da manema labarai ya fitar a yau da safennan, don bikin zagayowar ranar dimokuradiyya, Yusuf Olaniyonu, yace shugaban majalisar dattijan na kasa, Mr. Bukola Saraki, ya rattaba cewa, sai mutanen Najeriya sun dage da habaka tattalin arziki ne zasu sami ci gaban dimokuradiyya.

Shugaban, ya ce jinjina ta musamman ga talakawa 'yan Najeriya da suka zabo su, kuma suka yi ta hakuri dasu har aka kawo wannan lokacin.

KU KARANTA KUMA: 'Yadda rashin lafiyar Buhari ke taimakon tattalin arzikin Najeriya'

Mu taru mu ceci tattalin arzikin kasar mu, inji Bukola Saraki

Mu taru mu ceci tattalin arzikin kasar mu, inji Bukola Saraki

Ya kuma yaba da yadda abubuwa ke wakana a harkar hadin kai na 'yan kasa.

A wasikar, ya bada tabbacin dagewarsu wajen fitar da tsari na dokoki da zasu taimaki al'umma. Shekaru 18 dai ana dana dimokuradiyya tun korar sojoji daga mulki.

A wani al'amari na daban NAIJ.com ta rahoto Reno Omkri dai, dan adawa da ya rena Buhari, yace rashin lafiyar shugaba Buharin wai ai alheri ne ga tattalin arzikin Najeriya, ya kuma ce ai ma shugaba mai gwajin mulki Osinbajo yafi uban gidan nasa iyawa, don haka a bar masa mulki yafi alheri.

An samu rahoton cewa an jiyo Reno na babatu a jihar Florida ta Amerika, inda yake zaman labewa domin jiran karbar mulki daga APC, Mr. Reno, ya ce tadiya ce ga mukaddashi Osinbajo wai a cire sunan mukaddashi a kira shi da mai tsara yadda gwamnati zata kasance, kamar yadda wasikar Buhari ta karshe ta bayyanar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel