'Yadda rashin lafiyar Buhari ke taimakon tattalin arzikin Najeriya'

'Yadda rashin lafiyar Buhari ke taimakon tattalin arzikin Najeriya'

- Reno Omokri ya rena jam'iyyar APC

- Reno Omokri tsohon mai baiwa shugaba Jonathan shawara ne

- Reno baya shiru a kan batun siyasar Najeriya, ya wallafa littafi kan yadda mulkin Goodluck Jonathan ya kasance

Reno Omkri dai, dan adawa da ya rena Buhari, yace rashin lafiyar shugaba Buharin wai ai alheri ne ga tattalin arzikin Najeriya, ya kuma ce ai ma shugaba mai gwajin mulki Osinbajo yafi uban gidan nasa iyawa, don haka a bar masa mulki yafi alheri.

NAIJ.com ta samu rahoton cewa an jiyo Reno na babatu a jihar Florida ta Amerika, inda yake zaman labewa domin jiran karbar mulki daga APC, Mr. Reno, ya ce tadiya ce ga mukaddashi Osinbajo wai a cire sunan mukaddashi a kira shi da mai tsara yadda gwamnati zata kasance, kamar yadda wasikar Buhari ta karshe ta bayyanar.

KU KARANTA KUMA: Najeriya na fuskantar yiwuwar ballewa, inji fasto Tunde Bakare

Yada rashin lafiyar Buhari ke taimakon tattalin arzikin Najeriya'

Yada rashin lafiyar Buhari ke taimakon tattalin arzikin Najeriya'

A cewarsa, 'Buhari na tafiya asibiti sai naira ta farfado, da ya dawo sai ta noqe. Tattalin arziki ma da ya farfado ta hannun Osinbajo, in shugaba Buharin ya baro asibiti sai ya ruguje, don haka ina kira gare ku shuwagabannin tabo na duniya, ku mara wa Osinbajo baya ya tafiyar da Najeriya.

Buhari dai yana asibiti a karo na biyu na jinyar da yake fama da ita, kuma kusan duk shekararnan bayyi aiki ba, saboda rashin lafiya.

Saura dai shekaru biyu wa'adin mulkin jam'iyyar APC din yazo karshe.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel