Yadda wata mata ta sayar da yaranta 4 ba tare da sanin mijinta ba

Yadda wata mata ta sayar da yaranta 4 ba tare da sanin mijinta ba

Jami’an yan sandan Area M Command, Idimu sun damke wata mata wacce ta sayar da yaranta guda 4 a jihar Legas.

Game da cewar PM express, matar ta sayar da yara 4 cikin yaranta 5 ga mutane daban-daban ba tare a sanin mijinta ba.

Wata kara da mijin ya kai ofishin ne ya sanya ACP Austines Akika, ya sa aka damke matan mai suna Vicky.

Yan sanda su bayyana cewa tana sayar da yaran da daya bayan daya kuma ta samu nasarar sayar da 4, saura 1.

Yadda wata mata ta sayar da yaranta 4 ba tare da sanin mijinta ba

Yadda wata mata ta sayar da yaranta 4 ba tare da sanin mijinta ba

Yan sandan sunce Vicky tayiwa mijinta karya cewa ta kaisu wajen danginta ne har sai da mijin ya gano cewa sayar da su tayi.

KU KARANTA: Gwamnoni 8 da ake tabo idon talakawansu

Asirinta ya tonu ne bayan ta sayar da na hudun a kudi N400,000, kuma wani makwabci ya sanar da mijin.

Shi kuma ya kai kara ofishin yan sanda inda aka garkame ta. Ta bayyana gaskiyar magana kuma a yanzu ana kokarin gano inda yaran suke.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel