Yan Najeriya sun gamsu da kamun ludayin gwamnatin mu – Osinbajo

Yan Najeriya sun gamsu da kamun ludayin gwamnatin mu – Osinbajo

- Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya zayyano nasarorin gwamnatin Buhari

- Wasu daga cikin nasarorin da sun hada a yaki da cin hanci da rashawa

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya zayyano wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu tun bayan shekaru biyu da ta dare karagar mulki.

A cikin jawabinsa da Jaridar Premium Times ta samu, Osinbajo ya bayyana wasu cikin nasarorin da suka hada a yaki da cin hanci, yaki da ta’addanci da kuma samar da ayyukanyi ga matasa ga mata irin su N-Power da kuma ciyar da daliban Firamari.

KU KARANTA: Watan Azumi: Likita na gudanar da aiki kyauta a Asibiti

“Gwamnatin mu tayi kudurin magance manyan matsalolin Najeriya guda 3, tsaro, rashawa da tattalin arzikin kasa. Maganan gaskiya, tattalin arziki ya zame mana kalubale babba.” Inji Osinbajo.

Yan Najeriya sun gamsu da kamun ludayin gwamnatin mu – Osinbajo

Osinbajo

Osinbajo ya bayyana cewar gwamnatinsu ta samu kasar nan daure da matsalar Boko Haram, musamman a yankin Arewa maso gabas, inda yace sun sauya shuwagabannin Soji dake yaki da yan ta’addan tare da kara hadin gwiwa da makwabtan Najeriya, kuma an samu gagarumar nasara, inda a yanzu an gurgunta kungiyar.

Sa’annan ga nasarar da aka samu wajen kwato yan matan Chibok da kuma sako wasu da Boko Haram tayi bayan shiga yarjejeniya da tayi da gwamnati, bugu da kari Osinbajo yace sama da yan gudun hijira miliyan 2 sun koma gidajensu a shekaru 2 da suka gabata.

Wani nasarar gwamnatin Buhari da Osinbajo ya bayyana shine samar zaman lafiya a yankin Neja Delta ta hanyar tattaunawa da al’ummar yankin domin su daina fasa bututun man da kasar ta dogara da shi.

Sai bangaren yaki da cin hanci da rashawa, inda majiyar NAIJ.com tace Osinbaji yace gwamatinsu ta dage wajen gurfanar da mutanen da ake zargi da rashawa da satar kudin al’umma, sa’annan suna karfafa bangaren shari’a don gudanar da ayyukansa cikin sauki ba tare da son rai ba.

A bangaren habbaka tattalin arziki kuwa, Osinbajo yace lallai suna fuskantar kalubale babba, sakamakon halin da suka tsinci tattalin arzikin kasar, amma a nan ma ya bada tabbacin gwamnatinsu ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta samar da yanayin tattalin arziki mai kyau.

Daga karshe Osinbajo ya bukaci yan Najeriya dasu dage wajen yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’ar samun sauki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Osinbajo yayi bayani dangane da Biafra

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel