Dangantakar dake tskanina da gwamna Tambuwal – Obasanjo

Dangantakar dake tskanina da gwamna Tambuwal – Obasanjo

- Olusegun Obasanjo ya bayyana alakarsa da gwamnan jihar Sakkwato

- Obasanjo yace Tambuwal ya zamto Kaakakin majalisa bada san ran shi Obasanjon ba

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda gwamnan jihar Sakkwato Abubakar Tambuwal ya samu shiga zuciyarsa sosai, musamman a lokacin daya zama Kaakakin majalisar tarayya, inji jaridar Daily Trust.

Obasanjo ya bayyana cewar Tambuwal ya zamto Kaakakin majalisa duk da cewa bada san ran shi Obasanjon ba, toh amma bayan ya dare kujerra Kaakakin ne sai ya samu soyayyar Obasanjo saboda yadda ya tafiyar da kujerar.

KU KARANTA: Gwamna Tambuwal zai baiwa dalibai 20,000 kudin tallafin karatu

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Obasanjo yana fadin haka yayin taron cibiyar cigaban matasa na tsohin shugaban kasa Obasanjoda aka shirya don tattauna makomar matasan Najeriya, inda Obasanjo bayyana Tambuwal a matsayin daya daga cikin matasan Najeriya da suka samu nasara a siyasa.

Dangantakar dake tskanin da gwamna Tambuwal – Obasanjo

Tambuwal, Sultan da Obasanjo

“Gwamna Tambuwal, kasan lokacin da ka zama Kaakain majalisa ba da son raina bane, saboda ba haka jam’iyyar PDP ta shirya ba. Don haka lokacin da kazoo gare ni na fada maka ba kai bane matsalar, PDP ce matsalar.” Inji Obasanjo

Obasanjo ya kara fadin “Sa’annan na fada maka na ji dadin rahotannin da nake samu dangane da yadda kake tafiyar da majalisar wakilai a lokacin, kuma har yanzu ina samun gamsassun rahotannin ayyukan da kake yi a jihar Sakkwato. Kana daya daga cikin matasa da suka samu nasarar a siyasance.”

Dangantakar dake tskanina da gwamna Tambuwal – Obasanjo

Tambuwal da Obasanjo

Sai dai Onasanjo ya bayyana damuwarsa game da karuwar yawan matasan Afirka, inda yace “Babban damuwata ga yawan matasan mu, shine idan suka fusata”

Dangantakar dake tskanina da gwamna Tambuwal – Obasanjo

Tambuwal – Obasanjo

A nasa jawabin, Tambuwal yace bai kamata a cigaba da kiran matasa da sunan shuwagabannin gobe ba, ba tare da an samar musu wasu tsare tsare da zasu shirya su kama madafan iko ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicn darajan naira da dala

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel