Har yanzu kuna bukata na, kada kuyi mini fatan mutuwa - Obasanjo

Har yanzu kuna bukata na, kada kuyi mini fatan mutuwa - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, a ranan Lahadi ya baiwa matasa shawaran cewa su daina fatan mutuwansa da sauran dattijai.

Ya bayar da wannan shawara ne a taron shugabancin matasa da kwamitin cigaban matasa da dakin karatun shugaba Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, jihar Ogun.

Obasanjo wanda ya siffanta koke-koken da mutane keyi saboda kuncin rayuwa , ya baiwa matasa shawara kada su fidda rai.

Game da cewar Obasanjo, “Kada kuyi mana fatan mutuwa; kada kuyi mana fatan mutuwa saboda kuna bukatan mu. Kuna bukatan mu domin ilmantar da ku akan gobe. Kuna bukatan kwarewa da taimakon wasun mu domin shiriya a rayuwa.”

Har yanzu kuna bukata na, kada kuyi mini fatan mutuwa - Obasanjo

Har yanzu kuna bukata na, kada kuyi mini fatan mutuwa - Obasanjo

“Kada ku fidda tsammani, kada kuyifushi. Duk lokacin da na tafi kasar waje, sun tambayata menene abind nafi tsoro game da Najeriya da Afrika, sai in fada musu fushin matasa.”

KU KARANTA: An kammala aikin ruwan Zariya

“Munada Boko Haram a arewa, MASSOB da IPOB a kudu maso gabas, yan bindiga a Neja Delta, OPC a kudu maso yamma. Duka wannan sakamakon fushin matasa.”

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel