Najeriya na fuskantar yiwuwar ballewa, inji fasto Tunde Bakare

Najeriya na fuskantar yiwuwar ballewa, inji fasto Tunde Bakare

- Fasto Bakare mutumin Buhari ne, ya yi takara a matsayin mataimaki a tsohuwar jam'iyyar CPC a 2011

- Faston ya ce lallai dole a tsayar da haren haren makiyaya kan jama'a in ana son zaman Najeriya

A bikin cikar mulkin shugaba Buhari shekaru biyu, shugaban cocin Latter day Assembly da ke Legas, fasto Tunde Bakare, yace lalle a duba matsalar manoma-makiyaya in dai ana son kasar nan ta dore a matsayin kasa daya.

Mr. Bakare dai na wannan jawabi ne a jiya lahadi, a cocinsa ga mabiyansa, yace muddin ana so kasar nan ta zauna lafiya to a duka koke koken jama'ar kudanci da gabashin kasar nan, musamman batun fulani makiyaya da ke kai hare-hare.

KU KARANTA KUMA: Gwamnoni takwas da ke da tabo a idon talakawansu

Najeriya na fuskantar yiwuwar ballewa, inji Pasto Tunde Bakare

Najeriya na fuskantar yiwuwar ballewa, inji Pasto Tunde Bakare

A cewarsa, "Idan fa aka bari mutane suka tashi ramawa, to lalle zamu koma yakin basasa muyi ta kashe kawunanmu."

NAIJ.com ta tattaro cewa sami karin yawan hare-hare daga makiyaya akan mutane da kauyuka tun bayan hawan shugaba Buhari mulki, wanda shima fulani ne.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Najeriya sun koka kan rashin sanin madafa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel