Damukaradiyya a Najeriya: Ina aka baro kuma ina aka kama hanya?

Damukaradiyya a Najeriya: Ina aka baro kuma ina aka kama hanya?

– Damukaradiyyar Najeriya ta balaga a halin yanzu

– Sau biyu Soji na yin katsalandan a harkar siyasa

– Tun daga 1999 farar hula ke mulkin kasar nan

Yanzu dai ba shakka Damukaradiyya tayi karfi a Najeriya

A baya dai sau biyu Sojoji na kifar da Gwamnatin farar hula

An yi haka a shekarar 1966 da kuma 1984

Damukaradiyya a Najeriya: Ina aka baro kuma ina aka kama hanya?

Sojoji su ka kifar da Gwamnatin Shagari na farar hula

Muhammad Malumfashi na NAIJ.com ya rubuta wannan a Yau da ake bikin murnar Damukaradiyya a Najeriya.

KU KARANTA: Ana shirin tsige Gwamnan Jihar Kogi?

Damukaradiyya a Najeriya: Ina aka baro kuma ina aka kama hanya?

Damukaradiyyar Najeriya ta balaga bayan shekaru 18

Ka iya cewa Damukaradiyyar Najeriya ta balaga bayan an yi shekaru 18 ana bugawa babu tangarda. Ana kuma sa ran cewa abubuwa ma sai dai kyau kurum za su kara duk da cewa an fara jin kishin-kishin din juyin mulki, sai dai kamar 2010, babu inda yunkurin zai kai.

A rana irin ta yau a shekarar 1999. Janar Abdussalami Abubakar ya mikawa tsohon shugaba a mulkin Soja Janar Olusegun Obasanjo mulki. Har yau kuma tana hannun farar hula inda mutanen kudu su kayi kusan shekaru 14 inda ‘Yan Arewa su ka yi mulkin shekaru 4.

KU KARANTA: Inyamurai sun koka da halin siyasar Najeriya

Damukaradiyya a Najeriya: Ina aka baro kuma ina aka kama hanya?

Damukaradiyya a Najeriya ta gawurta

Akwai maganar cewa Shugaba Obasanjo ya nemi ya zarce fiye da wa’adin sa, uwar-bari dai ta sa dole ya kakaba tsofaffin Gwamnoni Marigayi Ummaru ‘Yaradua da Goodluck Jonathan. Bayan rashin lafiya ta kashe Ummaru ‘Yaradua ne Jonathan ya dare mulkin kasar har ya zarce.

An samu hadakar Jami’iyyun adawa inda su ka yi kutun-kutun su ka tika Shugaba Jonathan da kasa. Jam’iyyar APC ta Muhammadu Buhari ta karbi mulki wanda kawo yanzu shugaban kasar da wasu tulin alkawuran da APC ta dauka na kwance. Tuni dai har wasu sun fara hangen 2019!

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Tsohon Shugaban kasa Obasanjo a wani taro yana jawabi [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel