Ba sai an sake tsara Najeriya ba zata gyaru, inji limamin coci

Ba sai an sake tsara Najeriya ba zata gyaru, inji limamin coci

- Masu son a sake tsara Najeriya sun hada da tsohon mataimakin Obasanjo Atiku Abubakar

- Ana son a sake tsarin yadda Najeriya take don farantawa masu son ballewa rai

A ci gaba da kiraye kiraye da maida martani kan ko ya dace kasar Najeriya taci gaba da zama a matsayin kasa daya, ko kuma a sake komawa kan yadda ake a da, na cewa a maida gundumomin bangarorin kasar yadda suke a jihohi, mabambantan ra'ayoyi na kara fitowa daga masu tsokaci.

Wani limamin cocin Roman Katolika, Kayode Odetoyimbo, yace ba wannan ne zai magance rashin ta-ido daga jama'a ba, ba kuma hakan ne zai warware matsalolin da kasar ke ciki ba, ya yi nuni da cewa, sai an hada kai, an manta banbanci dake tsakanin al'ummu sannan ne za'a sami yadda ake so.

KU KARANTA KUMA: ‘Ka ji kunya’ – Fani-Kayode ya kai hari ga Adamu Adamu domin ya yi hidima a gwamnatin Buhari

Padan yace lalle akwai rashin sanin ya kamata a al'umma, shi yasa ake yawan samun batutuwa na cin hanci da rashawa a fadojin gwamnatoci dama tsakanin jama'a, a cewarsa, "Idan a yau kace na dena cin rashawa, hakan ta zauna, in kace ni malami an deba a makaranta ta, zai yiwu, in shugaba ko dan siyasa ma ya fadi hakan, to za'a iya ganin an dena rashawa".

NAIJ.com ta tuna cewa a dai baya-bayan nan, da yawa mutane kan nuna cewa matsalolin kasar yana kan shuwagabanni, amma kowa baya duba irin gudummawarsa a cikin samar da matsalar.

Wasu na ganin sai an sake tsara yadda Najeriya take ne abubuwa zasu gyaru.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel