‘Ka ji kunya’ – Fani-Kayode ya kai hari ga Adamu Adamu domin ya yi hidima a gwamnatin Buhari

‘Ka ji kunya’ – Fani-Kayode ya kai hari ga Adamu Adamu domin ya yi hidima a gwamnatin Buhari

- Femi Fani-Kayode ya kai hari ga ministan ilimi, Adamu Adamu kan aiki tare da gwamnati mai ci

- A cewar sa kamata ya yi a ce ministan ya nemi hanyar tsirar da shugaban sa Zakzaky da matarsa Zeenat

- Ya ce ministan na ilimi, Adamu Adamu ya ji kunya

Tsohon ministan dake kula da sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya kai hari ga ministan ilimi, Adamu Adamu kan aiki tare da gwamnati dake “kashe-kashe da kuma rufe musulman Shia a gidan yari.

NAIJ.com ta tuna cewa shugaban kungiyar musulman Shi’a na Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat na rufe a hannun hukumar DSS.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya yi kira ga sadaukarwa, da kuma yi ma Buhari addu’a a cikin sakon ranar demokradiyyaOsinbajo ya yi kira ga sadaukarwa, da kuma yi ma Buhari addu’a a cikin sakon ranar demokradiyya

Fani-Kayode ya ce maimakon aiki tare da gwamnati, ya kamata a ce ministan ilimin ya nemi hanyar da zai sa a saki shugaban sa da matarsa.

‘Ka ji kunya’ – Fani-Kayode ya kai hari ga Adamu Adamu domin ya yi hidima a gwamnatin Buhari

Fani-Kayode ya kai hari ga Adamu Adamu domin ya yi hidima a gwamnatin Buhari

Ya rubuta a shafin san a twitter, “Adamu Adamu ya kasance ministan ilimi.

“Shi mabiyin addinin Shi’a ne. ta yaya zai yi hidima a gwamnatin dake kisan kiyashi ga ‘yan uwansa mabiya Shi’a sannan kuma ta makantar da shugaban su sannan ta rufe shi da matar sa ba bisa ka’ida ba. Ya ji kunya!

“Fadar Allah ne ayi yaki don neman yancin kai, daidaito da kuma adalci. Abunda ya wajaba a kanmu kawai shine “Karda muyi amfani da fada da zubar da jini.”

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel