Koci Luis Enrique ya bar Barcelona da kofi

Koci Luis Enrique ya bar Barcelona da kofi

– Kungiyar Barcelona ta dauki kofin Copa Del Rey

– Barcelona ta doke Alaves a wasan karshe

– Wasan ne na karshe da Koci Enrique ya horas

Barcelona ta samu daga kofi a kakar bana.

Luis Enrique yayi ban-kwana da Barcelona.

Dan wasa Messi ya kara nuna kan sa a wasan.

Koci Luis Enrique ya bar Barcelona da kofi

Barcelona ta dauki kofin Copa Del Rey

Kungiyar Barcelona ta doke Alaves a wasan karshe a Gasar Copa Del Rey inda ta samu lashe kofin. Wannan ne wasa na karshe da mai horas da ‘Yan wasa Luis Enrique ya buga da kungiyar bayan ya dauki kofi 9 cikin shekaru 3.

KU KARANTA: Kocin Arsenal Wenger ya bar tarihi a Ingila

Koci Luis Enrique ya bar Barcelona da kofi

Barcelona ba ta tashi a banza ba a kakar bana

A shekarar farko dai Enrique ya dauki kusan dukkanin kofin da ya buga, a bara kuma ya lashe kofi biyu na gida. Bana dai Kocin ya tashi ne kurum da Gasar Copa Del Rey, inda su ka raba Jiha da Kungiyar. Messi yayi fice a wasan inda ya ci ya kuma ba da aka ci.

A Ingila kuma kun ji cewa Arsene Wenger ya zama Kocin da ya fi kowa lashe kofin FA na kasar shekaran jiya bayan ya dauko kofin sa na 7. Wenger ya dauki kofin sau 3 kenan cikin shekaru 4 da su ka wuce wanda ya sa Arsenal ta fi kowa yawan kofin na FA har 13.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ina mai shirin rage nauyi; teba tayi yawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel