Muhimmancin shan ruwa da Gwaiba a watan Azumin Ramadan

Muhimmancin shan ruwa da Gwaiba a watan Azumin Ramadan

- Masana sun bayyana amfanin cin gwaiba a watan Ramadan

- Muhimman amfanin Gwaiba sun da taimakwa wajen rage kiba

Sanannen abu ne a Musulunce cewar shan ruwa da kayan marmari abu ne mai kyau, wasu daga cikin kayayyakin marmarin sun hada da Lemu, Kankana, Abarba, Gwayba da sauransu.

A yau NAIJ.com ta kawo muku wasu muhimmancin amfani da Gwaiba a watan Ramadan ga mai Azumi, daga cikinsu akwai:

KU KARANTA: Watan Azumi: Likita na gudanar da aiki kyauta a Asibiti

Maganin ciwon daji:

Gwaiba na maganin ciwon daji, wato Cancer, sakamakon yana dauke da sinadarin Lycopene, shi wannan sinadari yana bada kariya daga cutar dajin mara da na nono.

Muhimmancin shan ruwa da Gwayba a watan Azumin Ramadan

Gwaiba

Nika abinci:

Jama’a da dama suna yawan fama da kwannafi da atini a watan Azumi sakamakon cin abinci dayawa, toh gwaiba na taimakawa wajen nika abincin da mutum yaci yadda ya kamata don yayi amfani a jikin mutum ba tare da ya sanya ka gudawa ba.

Rage Kiba:

Haka zalika Gwaiba na sanya rage kiba tare da inganta lafiyar kwakwalwa sakamakon Vitamin B3 da B6 dayake dauke da shi.

Gyaran Ido:

Bugu da kari masana sun tabbatar da Gwaiba na gyara ganin da idanu tare da inganta lafiyar idon kansa

Muhimmancin shan ruwa da Gwaiba a watan Azumin Ramadan

Lemun Gwaiba

Maganin Hawan jini da ciwon siga:

Yawan cin gwaiba na taimakawa wajen kona kitse da rage shi daga jikin mutum, sa’annan yana tsotse siga a jikin mutum don kare shi daga cutar siga.

Gyaran fata:

Gwaiba na daya daga cikin kayan marmarin dake gyara fatan jiki, da hana tsufa da wuri, sa’annan yana taimakawa wajen warkar da ciwo da wuri, kamar su fashewar lebe da sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hanyar rage kiba

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel