Jama'ar kabilar Igbo na shirin zaman-gida gobe don tunawa da Biyafara.

Jama'ar kabilar Igbo na shirin zaman-gida gobe don tunawa da Biyafara.

- An bada belin Mr. Kanu an kuma gindaya masa sharudda na kar ya shiga taron jama'a

- An kulle Nnamdi Kanu shekaru 2 kenan

- Mr Kanu na son jama'ar Ibo su balle daga Najeriya

Jama'ar kabilar Igbo na shirin zaman-gida gobe, don tunawa da Biyafara. Su dai kabilar Ibo na ganin an ware su a harkokin mulki shekaru kusan sittin a kasar nan.

Shugaban kungiyar, Yarima Nnamdi Kanu ne yake fadin hakan, a bikin tunawa da shabbat, wato asabar, ta addinin yahudawa, da aka yi a gidansu, karshen makon nan.

A makalar da ya gabatar, a wurin taron, ya yi kira ga gwamnatin tarayya cewa dole su ajje ranar da za'ayi rafarandan, don jin ta bakin kabilar Ibo ko suna so su balle daga Najeriya ko kuwa zasu zauna, kamar dai yadda ake yi a sauran kasashe.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya yi kira ga sadaukarwa, da kuma yi ma Buhari addu’a a cikin sakon ranar demokradiyya

Yace in ko ba haka ba, bazasu kara yin kowanne zabe ba.

Jama'ar kabilar Igbo na shirin zaman-gida gobe, don tunawa da Bayafra.

Jama'ar kabilar Igbo na shirin zaman-gida gobe, don tunawa da Bayafra.

NAIJ.com ta ruwaito cewa a belin da aka bashi, an hana shi zama cikin taron da ya fi mutum goma, an kuma hana shi maganganu na siyasa, amma ya ki ji. Hasali ma, yace kasar Najeriya gidan namun daji ne.

KU KARANTA KUMA: An hurowa Gwamnan Legas wuta (Abin da ya faru zai ba ka mamaki)

Mr. Kanu na kara farin jini a idon jama'arsa, amma ba kowa ne ke goyon bayan irin akidarsa ta ayi yaki ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon NAIJ.com da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi jawabi a kan yakin biyafara:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel