An hurowa Gwamnan Legas wuta (Abin da ya faru zai ba ka mamaki)

An hurowa Gwamnan Legas wuta (Abin da ya faru zai ba ka mamaki)

– Mai girma Gwamnan Jihar Legas ya shiga cikin babbar matsala

– Gwamna Akinwumi Ambode ya tsige wani Malamin coci

– Ana zargi dai don kurum Malamin ya batawa matar sa rai ne aka sallame sa

Gwamna Ambode ya sallami Malamin coci a kan abin da bai kai ya kawo ba.

Hakan ta sa Jama’a su ka huro masa wuta.

An kira Gwamnan ya tuba ya nemi afuwa.

Gwamnan Jihar Legas ya tsige wani Malamin da ke kula da wani coci bayan wani dan abin da bai taka kara ya karya ba. Malamin dai ya batawa matar Gwamnan rai inda ta nemi ya fara ba ta tabarruki kafin kowa ya kuma ki yin hakan lokacin da ake ibada.

An hurowa Gwamnan Legas wuta (Abin da ya faru zai ba ka mamaki)

Gwamna Ambode da Matar Mai girma Gwamnan na Legas

KU KARANTA: Dangote da wasu Gwamnoni za su saye kamfanin Peugeot

Wasu sun ce a dalilin wannan ne aka kori Fasto Alausa Taiwo daga aiki ba tare da jin ta bakin sa ba. Wasu dai su na ganin Gwamnan bai kyauta ba sam inda su ka nemi ya sake duban lamarin a matsayin sa.

Kun ji cewa Sanata Dino Melaye da sauran wasu ‘Ya ‘yan Jam’iyyar sun kara taso Gwamnan Kogi a gaba cewa ya bar kujerar sa. Sai dai Gwamnan yace masu wannan maganar ma dai wasa su ke yi don sai dai su jira 2019.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hira da Jama'a game da zaman aure [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel