An nemi Bunsurun Najeriya a Amurka sama ko ƙasa an rasa

An nemi Bunsurun Najeriya a Amurka sama ko ƙasa an rasa

- Wani bunsurun Najeriya yayi batan dabo a Amurka

- Jmai'an hukumar yansandan Amurka sun shiga neman bunsurun afujajan

Jami’an hukumar yansandan garin Winnebago dake kasar Amurka ta fara neman barayin da suka saci wani Bunsurun Najeriya ruwa a jallo.

Kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito cewar abinda yafi tayar ma jami’an yansandan Amurka hankali shine wanene ya saci wannna Bunsuru dan Najeriya mai suna ‘Cinnamon’?

KU KARANTA: Ba ya jin garin nan: Dangote zai saye kamfanin Peugeot

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito hukumar Yansandan suna neman bunsurun wanda aka sace daga garin Poygan, wanda jama’an garin kwata kwata basu wuce 1,000, kamar yadda alkalumman kididdiga suka nuna.

An nemi Bunsurun Najeriya a Amurka sama ko ƙasa an rasa

Bunsurun Najeriya Cinnamon

Mamallakin Bunsuru Cinnamon, yace tun a ranar 25 ga watan Mayu ne aka saci Bunsuru Cinnamon, amma suna sa ran a dawo musu da shi lafiya.

Itama hukumar yansandan Winnebago ta bayar da lambar waya da za’a tuntuba ga duk wanda ya ga Bunsuru Cinnamon kamar haka +1-920-236-7300, inda ta kara da cewa Bunsurun ba shi da lafiya, yana samun kulawa yanzu haka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya zaki yi idan Mijinki na dukan ki?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel