Watan Azumi: Likita na gudanar da aiki kyauta a Asibiti

Watan Azumi: Likita na gudanar da aiki kyauta a Asibiti

- Wani Asibiti a jihar Kaduna ya sanya ganin Likita kyauta ga jama'a

- Shugaban Asibitin, yace yayi haka ne don samun albarkacin watan Ramadana

Wata asibiti mai zaman kanta a jihar Kaduna, Sultan Hospital karkashin jagoran Asibitin, Dakta Tasiu Ibrahim ta sanya ganin likita kyauta gaba daya watan Ramadan don sauwaka ma jama’a halin matsi a wannan wata mai alfarma tare da neman yardarm Ubangiji, Allah.

Shugaban Asibitin, Dakta Tasi’u Ibrahim ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya kara da cewa wasu cikin ayyukan jin kai da asibitin ta kudiri yi a wannan wata mai alfarma sun hada da sassauta kudaden manyan ayyuka kamar su tiyata da karbar haihuwa da kuma yin rangwame akan farashin magunguna.

KU KARANTA: Ba ya jin garin nan: Dangote zai saye kamfanin Peugeot

Sai dai ko a watan data gabata, sai da Asibitin ta gudanar da wani shirin bada magani kyauta ga masu cutar gyambon ciki (Ulcer), a nan ma shugaban Asibitin ta shirya wannan ne da sunan tunawa da kyawawan halayyar marigayi Alhaji Ahmadu Chanchangi.

Watan Azumi: Likita na gudanar da aiki kyauta a Asibiti

Likita Tasi'u yayin aikin bada magani kyauta

Sa’annan taron ya samu halartan babban Malami kuma Likita Sheikh Ahmad Gumi. Kafin nan ma sai da Asibitin Sultan ta shirya wani taro makamancin wannan don bada magani kyauta ga masu cutar diabetes da na hawan jini, wanda taron ya samu halartan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta wakilcin ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau.

Watan Azumi: Likita na gudanar da aiki kyauta a Asibiti

Dakta Gumi tare da Likita

Haka zalika NAIJ.com ta ruwaito Asibitin ta taba ware wata guda don ganin Likita kyauta don murnar dawowar shugaban kasa Muhamamdu Buhari daga kasar Ingila inda aka duba lafiyarsa a wancan lokaci.

Watan Azumi: Likita na gudanar da aiki kyauta a Asibiti

Dakta Gumi a karshen taron

Watan Azumi: Likita na gudanar da aiki kyauta a Asibiti

Shugaban Asibitin tare da Dambazau yayin bada maganin ciwon siga kyauta

Watan Azumi: Likita na gudanar da aiki kyauta a Asibiti

Mahalarta taron bada maganin gyambon ciki kyauta

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Dala zai karye kamar Naira?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel