Gwamnoni takwas da ke da tabo a idon talakawansu

Gwamnoni takwas da ke da tabo a idon talakawansu

- Ana bikin cikar wasu gwamnonin shekaru 2, wasu kuma shekaru 6 da hawa mulki

- Da yawan gwamnoni farin jinin shugaba Buhari ya kawo su, kuma har sun ginshi jama'arsu

A lokacin da wasunsu ke bikin cika shekaru biyu, da yawan gwamnoni na da wani tabo ko badakala da ake bincikar su ko zargin su a kai.

Wasu sun musanta, wasu kuwa sunyi biris da batun, ko menene suke yi da ke jawo musu bakin jini?

KU KARANTA KUMA: ‘Ka ji kunya’ – Fani-Kayode ya kai hari ga Adamu Adamu domin ya yi hidima a gwamnatin Buhari

Gwamnoni takwas da ke da tabo a idon talakawansu

Gwamnoni takwas da ke da tabo a idon talakawansu

NAIJ.com ta tattaro maku tarin gwamnonin dake fuskantar badakala:

1. Gwamna Abdul'aziz yari: Ana zarginsa da wawashe dala miliyan uku, $3m da gina katafaren otal a jihar Legas, duk da ya musanta hakan, ana zargin ya garzaya fadar shugaban kasa, ya tuba, tare da alkawarin dawo da kudin.

2. Gwamna Aminu Bello Masari: Ya sayo makara guda dubu 3, akan naira dubu arba'in kowacce, don raba wa masallatai, wannan ya jawo cece-kuce a katsina shin ko amfani da kudin gwwamnati ya kamata yayi ko na aljihunsa wurin neman lada.

3. A jihar Ribas ma gwamna Nyesom Wike ne ake zargi da kira, da kuma barazanar zai kashe wani ma'aikacin INECa lokacin zaben sanatocin jihar, zargin da ya musanta, duk da an sami rakoda na maganar, da kuwa makudan kudi tsirara miliyoyi domin ya saye zaben.

4. A Kogi ma dai hakan take, Gwamna Bello yayi rajistar zabe sau biyu, ya harzuka INEC, har ma dan gwagwarmaya Dino Melaye na kiran sa da ya bar mulki, yayi murabus, jam'iyyarsa ta APC ma tayi tir da shi.

5. A jihar Delta ma, ana zargin gwamna Okowa da mika wa budurwarsa dala miliyan goma domin ta boye masa a Amurka, ita kuwa ta tsere da kudin, yayi yayi ta dawo taki, sai dai cewa akayi ya kaita kara domin ceto kudin.

6. Gwamna Ambode ma dai na legas na shan suka wajen sauke limamin cocin jihar da yayi bisa fadan da yake yi da matar shi gwamnan, bayan da taje ibada amma ba'a bata muhimmiyar tarba ba, pasto dai ya rasa aikinsa a cocin gidan gwamnati.

7. A Kano ana zargin gwamna Ganduje da yawan bacci a taro, batun da ya musanta, ya kuma ce ai shi likimo yake ba bacci ba, abun da ya jawo muhawara tsakanon masoya da 'yan kwankwasiyya.

8. A jigawa ma dai ana fushi da gwamna Abubakar Talamiz, bayan ya karbe wa kauyawa gona, ya biya diyya amma wasu sunki karba, sun kuma kullaci wadanda suka amshi kudin, da ma ware su a al'umma, don kuntata musu da wargaza shirin, shirin dai na nufin mutanen China za'a bawa domin su yi noman rake don samar da siga da ma makamashin ethanol mai kama da fetur, domin habaka arzikin jihar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mulki ga mataimakin sa Yemi Osinbajo:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel