2017: Hukumar kula da aikin Hajji ta bayyana kudin kujera

2017: Hukumar kula da aikin Hajji ta bayyana kudin kujera

– Hukumar kula da aikin Hajji ta sanar da kudin kujerar wannan shekara

– NAHCON tayi wannan sanarwa ne a wani taron ta da tayi a Abuja

– Jihohi 6 sun bayyana nawa Mahajjata za su biya domin sauke farali

Jihohin Neja, Nasarawa, Katsina sun bayyana kudin kujerar aikin Hajjin bana

Haka kuma Jihohin Kano, Kaduna da Adamawa sun bayyana kudin kujerar.

Kudin kujerar aikin Hajjin bana dai ya haura Miliyan daya da rabi

2017: Hukumar kula da aikin Hajji ta bayyana kudin kujera

Musulmai zagaye da Ka'aba wajen sauke farali

Jihar Nasarawa za ta karbi N1, 544, 894.16 yayin da Jihar Neja za ta karbi N1, 525, 483.30. Kujera Jihar Kadua kuma tana kan N1, 535, 503.68 yayin da Mutanen Adamawa za su biya N1, 530, 101.08. Kusan dai kudin kujera a Jihar Nasarawa ya fi tsada.

KU KARANTA: Babban Shehin Malami ya soki mulkin Buhari a Tafsiri

2017: Hukumar kula da aikin Hajji ta bayyana kudin kujera

Kudin kujerar aikin Hajji ya haura Miliyan daya da rabi

A Jihar Kano dai kudin kujerar shi ne N1, 537, 859.97. Kusan dai kowane Mahajjaci zai biya N38,000 na yanka watau hadaya wanda ba a hada da shi cikin lissafin na bana ba. Za ayi amfani da bankin nan na Ja’iz ne wajen biyan kudin.

Kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya shirya sayen kamfanin PAN masu kera motoci. Gwamnatin Jihohin Kebbi da Kaduna ma za su saye wani hannun. Kamfanin Peugeot da ke Jihar Kaduna dai na iya kera motoci sama da 90,000 a shekara.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Akwai ranar da Dala za ta dawo daya da Naira?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel