Doka ta ba mu dama mu yi kari cikin kasafin kudi-Honarabul Onuigbo

Doka ta ba mu dama mu yi kari cikin kasafin kudi-Honarabul Onuigbo

– Wani Dan Majalisa yace su na damar su kara abin da ke cikin kasafin kudi

– A cewar sa kundin tsarin mulkin kasa ya ba su wannan damar

– Honarabul Sam Onuigbo ya bayyana wannan

Wani Dan Majalisar Jihar Abiya ya maidawa su Femi Falana martani.

Dan Majalisar yace suna iya kara kudin da ke cikin kasafi.

A cewar sa doka ta ba su damar wannan.

Doka ta ba mu dama mu yi kari cikin kasafin kudi-Honarabul Onuigbo

Honarabul Onuigbo na Majalisar Tarayya

Honarabul Sam Onuigbo, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Umahia da Ikwuano na Jihar Abiya yace kundin tsarin mulkin kasa ya ba su damar su kara ko rage wani abu da ke cikin kundin kasafin kudi.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gaza Inji Sheikh Gumi

Doka ta ba mu dama mu yi kari cikin kasafin kudi-Honarabul Onuigbo

Kasafin kudi: Majalisa na wuce gona da iri Inji masana

Dan Majalisar ya maidawa babban Lauyan nan Femi Falana martani ne bayan ya zargi Majalisar da cusa abin da ba a basu dama ba a kasafin shekarar 2017 da shugaban kasa Buhari ya aika masu. Honarabul Onuigbo yace ragewa da karawa duk wannan cikin aikin su ne.

Kwanaki wani tsohon Mataimakin Gwamnan babban bankin CBN yace dole a tantance aikin ‘Yan Majalisar kasar nan wajen kasafin kudi. Yace ‘Yan Majalisa ba su da hurumin cusa wani aiki ko kara kudin da ke cikin kasafin kudin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mukaddashin Shugaban kasa yana wani jawabi kwanaki [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel