Osinbajo ya yi kira ga sadaukarwa, da kuma yi ma Buhari addu’a a cikin sakon ranar demokradiyya

Osinbajo ya yi kira ga sadaukarwa, da kuma yi ma Buhari addu’a a cikin sakon ranar demokradiyya

- A yau Litinin, 29 ga watan Mayu ta yi daidai da ranar dimokuradiyya a Najeriya, sannan kuma ranar yi daidai da ranar da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya cika shekaru biyu da hawa karagar mulki

- Ana gudanar da bikin damokradiyya ta bana ne a daidai lokacin da shugaban kasar Buhari ke jinya a birnin Landan sakamakon wata rashin lafiya da ya ke fama da ita

- Mukaddashin shugaban kasar farfesa Yemi Osinbajo ya gabatar da jawabi gay an Najeriya a madadinsa

- Osinbajo ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’o’I domin samun sauki dangane da rashin lafiyar da ya ke fama ita a halin yanzu

Kamar ko wace shekara, yau Litinin, 29 ga watan Mayu ta yi daidai da ranar dimokuradiyya a Najeriya, sannan kuma ranar yi daidai da ranar da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya cika shekaru biyu da hawa karagar mulki.

Ana gudanar da bikin damokradiyya ta bana ne a daidai lokacin da shugaban kasar Buhari ke jinya a birnin Landan sakamakon wata rashin lafiya da ya ke fama da ita, sai dai mukaddashin shugaban kasar farfesa Yemi Osinbajo ya gabatar da jawabi gay an Najeriya a madadinsa.

A cikin Jawabin mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa guda uku da suka hada da tsaro da yaki da rashawa da kuma tattalin arzikin kasar.

KU KARANTA KUMA: Shekaru 2 a kan mulki: Babu wani abun da za’a yi wa murna a mulkin Buhari – Jam’iyyar PDP

NAIJ.com ta tattaro inda Mukaddashin shugaban kasar ya bayyana cewa ko shakka babu gwamnatin su ta yi nasara sosai ta fannin tsaro musamman yakin da ake yi akan kungiyar ‘yan ta’adda na Boko Haram, domin a yau ba wani yanki da ke karkashin ikon kungiyar, sannan sun yi nasarar ceto wasu daga cikin ‘yan Matan Chibok wadanda sace su ya tayar da hankulan kasa da ma duniy baki daya.

Ya kuma bayyana cewa an samu nasarar samar da tsaro a yankin Neja Delta mai arzikin mai, kamar yadda aka samu irin wannan nasara a fagen yaki da rashawa sakamakon samun goyo daga al’umma da ke tsegunta wa hukuma wadanda ke yi wa tattalin arziki zagon kasa.

Ya kuma danganta matsalar tattalin arziki a matsayin babban kalubalen da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskanta.

KU KARANTA KUMA: Doka ta ba mu dama mu yi kari cikin kasafin kudi-Honarabul Onuigbo

Osinbajo ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’o’I domin samun sauki dangane da rashin lafiyar da ya ke fama ita a halin yanzu.

Sannan ya yi kira ga samar da hadin kai a tsakanin ‘yan Najeriya baki daya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com a lokacin da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ke bayar da jawabi kan yakin Biyafara:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel