Shekaru 2 a kan mulki: Babu wani abun da za’a yi wa murna a mulkin Buhari – Jam’iyyar PDP

Shekaru 2 a kan mulki: Babu wani abun da za’a yi wa murna a mulkin Buhari – Jam’iyyar PDP

- Jam’iyyar PDP ta ce ba ta ga abin da za a yi wa murna ba a shekaru biyu da APC tayi tana mulkin kasar

- PDP ta ce gwamnatin Buhari bata tsinana wa al’ummar Najeriya komai ba in banda tsantsar wahala da ake sha a duk inda ka leka

Jam’iyyar PDP ta ce ba ta ga abin da za a yi wa murna ba a zagayowar ranar demokradiyya na wannan shekara a daidai lokacin da jam’iyyar APC karkashin jagoranci shugaba Muhammadu Buhari ta cika shekaru biyu a kan karagar mulki.

PDP ta ce gwamnatin Buhari bata tsinana wa al’ummar Najeriya komai ba in banda tsantsar wahala da ake sha a duk inda ka leka.

Kakakin jam’iyyar na bangaren Makarfi Dayo Adeyeye ne bayyanar da hakan a wata jawabi da jam’iyyar ta fitar.

Shekaru 2 a kan mulki: Babu wani abun da za’a yi wa murna a mulkin Buhari – Jam’iyyar PDP

Jam’iyyar PDP ta ce babu wani abun murna a gwamnatin Buhari

Yace su a jam’iyyar PDP basu ga abin da za ayi wa murna ba a tsawon shekaru biyu da jam’iyyar APC ta yi tana mulkan kasar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Buhari ka gaza - Cewar malamin musulunci ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da PDP da kuma APC

Ya ba da misalai inda ya kwatanta gwamnatin su na baya da wannan gwamnati na shugaba Muhammadu Buhari.

“A lokacin Mulkin PDP mun tafi mun bar dala ta na naira N190 amma yanzu dala ta kai naira N400. Mafi karancin albashin ma’aikacin gwamnati wanda naira N18,000 zai iya siyan akalla buhuhunan shinkafa biyu harda canji amma yanzu ina. Da buhun siminti na naira N1,700 ne amma yanzu naira N2,700 ne, da sauran abubuwa da dama."

Bayan ga haka NAIJ.com ta tattaro cewa jam’iyyar tayi magana akan harkar tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da wannan gwamnati ta sa a gaba sannan kuma tayi kira ga mataimakin shugaban kasa da ya gaggauta saka hannu a kasafin kudi ko a dan samu sauki a wahalhalun da mutane ke fama dashi.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com da ta tambayi 'yan Najeriya ko sun goyi bayan juyin mulki:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel