Kungiyoyin fafutukan kafa Biafra za su kauracewa bukukuwan demokradiya

Kungiyoyin fafutukan kafa Biafra za su kauracewa bukukuwan demokradiya

- Kungiyoyin fafutukan kafa Biafra a karkashin jagorancin Nnamdi Kanu sun yi farfagandan kaucewa bukukuwan ranar kafuwar demokradiyya

- Kungiyar ta umarni jami’an sa da su zauna a gidajensu lokacin bukukuwan.

- Ike Ekweremadu ya shawarci kungiyar da ta janye umarni kaucewa bikin demokradiyya

Masu fafutukan ganin an kafa kasar Biafra daga Najeriya sun bukaci ilahirin magoya bayansu a kasar da su kauracewa bukukuwan da za'ayi na ranar kafuwar demokradiyya a Kasar.

Sun bukaci jama'ar su dake yankin kudu maso gabashin kasar da su zauna a gidajensu lokacin bukukuwan.

KU KARANTA: Buhari ka gaza - Cewar malamin musulunci ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da PDP da kuma APC

NAIJ.com ta ruwaito cewa, tuni dai mukaddashin shugaban majalisar dattijai Ike Ekweremadu ya roki kungiyar da ta janye wannan umarni da ta baiwa jama'ar su.

Kungiyoyin fafutukan kafa Biafra za su kauracewa bukukuwan demokradiya

Kungiyoyin fafutukan kafa Biafra

Ike Ekweremadu na sukan ra'ayin masu fafutukan kirkiro kasar Biafran ne a wajen addu'oi da akayi ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu a garin Abakaliki

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali shugaban masu fafutukan kafa Biafra Nnamdi Kanu a lokacin da aka bada belin sa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan

Buhari ya taya Iran da Iraqi bakin cikin girgizan kasa da ya afku kwanan nan
NAIJ.com
Mailfire view pixel