Buhari ka gaza - Cewar malamin musulunci ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da PDP da kuma APC

Buhari ka gaza - Cewar malamin musulunci ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da PDP da kuma APC

- Babban malamin nan na addinin musulunci, Ahmed Abubakar Gumi, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gaza ma ‘yan Najeriya

- Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da suyi watsi da jam’iyyun APC da PDP baki daya

- Gumi ya bayyana cewa a gwamnatin shugaba Buhari, manyan jami’ai na tafiya da kudaden sata da kuma rashawa

Wani babban malamin musulumci Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa gwamnatin shugabna kasa Muhammadu Buhari ta gaza sosai.

Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayinda yake kimanta gwamnatin shugaban kasa Buhari da kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai ciki kin shekaru biyu da tayi a kan karagar mulki.

A cewar malamin, shugaban kasar da jam’iyyar sa basu yadda ake zata ba.

Malamin ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da suyi watsi da gwamnati mai ci wato APC da kuma jam’iyyar Peoples Democratic Party.

Buhari ka gaza - Cewar malamin musulunci ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da PDP da kuma APC

Sheikh Abubakar Gumi ya kalubalenci shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa ya gaza ma yan Najeriya

Sheikh Gumi ya kuma raina tsarin mulkin jam’iyyar mai ci a yanzu.

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta sayar da yara 4 cikin 5 ba tare da sanin mijinta ba

Da yake magana a kan cin hanci da rashawa, Gumi ya bayyana cewa ko a gwamnatin shugaba Buhari, manyan jami’ai na satar kudi da rashawa.

A halin yanzu, a ranar Asabar, 27 ga watan Mayu mukaddashin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya nada babban daraktan hukumar fansho.

NAIJ.com ta tattaro cewa Funso Doherty ne sabon shugaban da aka nada wanda yam aye gurbin Mal. Dikko Aliyu AbdulRahman.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel