Toh fa: Ana duba yiwuwar hana shiga jirage da na’ura kwamfuta

Toh fa: Ana duba yiwuwar hana shiga jirage da na’ura kwamfuta

- Kasar Amurka ta ce tana duba yiwuwar hana shiga jiragen sama masu zirga-zirga tsakanin kasa da kasa da na’ura kwamfuta

- John Kelly ya ce kasar na fuskantar barazanar hare-haren ta'addanci

- A cewar Kelly, 'yan ta'adda suna da burin ganin sun kakkabo jirgin sama, musamman na Amurka

Hukumomi a Amurka suna duba yiwuwar hana mutane shiga da kwamfutocin laptop cikin dukkan jiragen sama masu zirga-zirga tsakanin kasa da kasa, saboda barazanar hare-haren ta'addanci dake kasar ke fuskanta.

Shugaban hukumar tabbatar da tsaron cikin gida ta Amurka, John Kelly, ya ce akwai tabbatacciyar barazanar hare-haren ta'addanci a bangaren jiragen sama na kasar, a don haka, a kwai yiwuwar zai aiwatar da matakin hanin.

KU KARANTA: Bayan tafiyar Buhari: Osinbajo yayi sababbin nade-nade

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Kelly ya ce 'yan ta'adda suna da burin ganin sun kakkabo jirgin sama, musamman ma na Amurka, yayin da yake cikin tafiya a sama.

Toh fa: Ana duba yiwuwar hana shiga jirage da na’ura kwamfuta

Jirgin sama ta kasar Amurka

Dama dai Amurkan ta hana fasinjoji dake tasowa daga wasu kasashe goma, akasarinsu daga Gabas ta Tsakiya, shiga jiragen sama da kwamfutocin na laptop.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ra'ayoyin 'yan Najeriya kan komawar shugaba Buhari Landan don duba lafiyarsa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel