Wata mata ta sayar da yara 4 cikin 5 ba tare da sanin mijinta ba

Wata mata ta sayar da yara 4 cikin 5 ba tare da sanin mijinta ba

- An kama wata mata a jihar Lagas kan zargin cewa ta sayar da ‘ya’yanta

- An rahoto cewa matar gidan mai suna Vicky ta sayar da hudu daga cikin ‘ya’yanta biyar sannan kuma ta yi wa mijinta karya

- Asirinta ya tonu ne bayan ta siyar da na karshem kan N400,000 sannan kuma wata makwabciyar ta ta sanar da mijin

Jami’an ‘yan sanda sun kama Misis Vicky, wata matar gida a Lagas kan zargin cewa ta sayar da hudu daga cikin ‘ya’yanta biyar ga mutane daban-daban ba tare da sanin mijinta ba.

Mijinta ya aika takarda ga shugaban ‘yan sandan yankin ACP Austines Akika sannan kuma y aba jami’an ‘yan sanda umurnin kama ta.

KU KARANTA KUMA: An daura auren Ahmed Musa da sabuwar matar sa Juliet Ejue

Wata mata ta sayar da yara 4 cikin 5 ba tare da sanin mijinta ba

Wata mata ta sayar da yara 4 cikin 5 ba tare da sanin mijinta ba

A cewar PM Express, tana sayar da yaran ne daya bayan daya sannan kuma ta yi nasaran sayar da hudu daga cikin yaran.

Da farko, ta yi ma mijinta karyan cewa ta kai yaran gurin ‘yan’uwansu ne har sai lokacin da mijin ya gano daga baya cewa tana sayar da yaran ne.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ta sayar da na karshen a kan N400,000 sannan makwabta suka sanar da mijin wanda ya kai kara gidan ‘yan sanda aka zo aka kamata sannan aka tsare ta a kurkuku.

An rahoto cewa ta rigada ta fada ma ‘yan sanda gaskiya yayinda ake kokarin ceto yaran sannan kuma a kama wadanda suka siya yaran.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel