Babbar kotun tarayyya za ta yanke hukunci kan batun sauyawa Sule Lamido alkalin dake jagorantar shiri'arsa da EFCC

Babbar kotun tarayyya za ta yanke hukunci kan batun sauyawa Sule Lamido alkalin dake jagorantar shiri'arsa da EFCC

- Kotun kolin Najeriya zata yanke hukunci kan batun sauyawa tsohon gwamnan jihar Jigawa alkali a ranar 7 ga watan Yuli

- Ana zargin tsohon gwamnan ne da wasu ‘ya ‘yansa biyu da yin wawashe da dukiyoyin al'umma

- Mutanen uku sun dage akan mai shari'a Adeniyi Ademola ya cigaba da yi musu shari'a

Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a birnin Abuja ta tsaida ranar 7 ga watan Yuli domin yanke hukunci akan bukatar da tsohan gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido da 'ya'yansa biyu Mustapha da Aminu suka gabatar na kalubalantar sake sauya musu alkalin dake shari'ar zargin wawashe dukiyoyin al'umma da ake yi musu.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, hukumar EFCC da ta gabatar da zarge -zarge 27 akan mutanen 3, ta ki amincewa da mayar da shari'ar zuwa babban mai shari'a na birnin tarayya Abuja mai sharia B.O. Quadri maimakon mai shari'a Ibrahim Auta.

KU KARANTA: Yajin aikin Malaman makaranta ya sa Kwamishinoni za su shiga aji

Wadanda ake zargi sun dage akan mai shari'a Adeniyi Ademola ya cigaba da yi musu shari'a.

Bisa karfin ikon da babban mai shari'ar yake da shi ya mayar da sauraran karar ga wani sabon alkali bayan da aka kama mai shari'a Ademola bisa zargin cin hanci da rashawa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin

cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel