Dan wasan Man United Paul Pogba ya je aikin Umarah (HOTUNA)

Dan wasan Man United Paul Pogba ya je aikin Umarah (HOTUNA)

- Dan wasan kwallon kafa ta kungiyar Manchester United Paul Pogba ya tafi kasar Saudiyya don fara aikin Umarah

-Ya tafi kasar Saudiyya ne domin ya godewa Allah kan tarin nasarar da suka samu a bana

- Ya kuma taya musulmai murnar shiga wata mai tsarki ta Ramadan

Dan wasan kwallon kafa ta kungiyar Manchester United Paul Pogba ya tafi kasar Saudiyya don fara aikin Umarah a wata mai tarin albarka wato watan Ramadan, 'yan kwanaki kadan bayan kulob dinsa ta lashe kofin Gasar Europa.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram a ranar Asabar, Pogba ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Makkah domin godewa Allah kan tarin nasarar da suka samu a bana.

KU KARANTA KUMA: An daura auren Ahmed Musa da sabuwar matar sa Juliet Ejue

Dan wasan Man United Paul Pogba ya je aikin Umarah (HOTO)

Dan wasan Man United Paul Pogba ya je aikin Umarah

Hakazalika, a ranar Lahadi ya wallafa wani bidiyo a shafin wanda yake nuna shi a tsaye a gaban Harami. Kuma sabanin yadda aka saba ganinsa a filin wasa, Pogba ya sauya irin salon askinsa.

Dan wasan wanda da ma Musulmi ne, ya ce yana yi wa Musulmai barka da azumi.

KU KARANTA KUMA: Ahmed Musa da budurwar sa Juliet sun saki hotunan aurensu

NAIJ.com ta samu labarin cewa Pogba, wanda ya kasance dan asalin kasar Faransa ne, yana yin ibadarsa ta addinin Musulunci.

Pogba ya koma United a bara daga Juventus a matsayin dan wasan da ya fi kowanne tsada a duniya.

NAIJ.com ta tattaro maku sauran hotunan Paul Pogba a kasar Saudiyya:

Dan wasan Man United Paul Pogba ya je aikin Umarah (HOTO)

Dan wasan Man United Paul Pogba a cikin harami

Dan wasan Man United Paul Pogba ya je aikin Umarah (HOTO)

Dan wasan Man United Paul Pogba ya je aikin Umarah

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon yan wasa a lokacin da suke shirin zuwa wani wasa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel