Shaikh Zakzaky ya raba abinci ga mabukata don Ramadana a Zariya (Hotuna)

Shaikh Zakzaky ya raba abinci ga mabukata don Ramadana a Zariya (Hotuna)

- Shaikh Ibraheem Zakzaky ya rabawa al’umma musulmai mabukta a garin Zaria kayayyakin abinci don tallafa masu a wannan watan Ramadana

- Kayan abincin sun hada da shinkafa, masara, gero, suga ,taliya da dai sauran su

- Zakzaky ya umuni wani dan uwansa da ya jagoranci raba kayan tallafin ga mabukata

- An fara rabon tallafin ne tun daga ranar Talatar da ta gabata

Kamar yadda ya saba a duk shekara a lokaci irin wannan watan Ramadana, jagoran harkar musulunci a Najeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky na raba kayan abinci ga mabukata a duk lokacin da watan Ramadana ya gabato. Kayan abincin wanda suka hada da shinkafa, masara, gero, suga ,taliya da dai sauran su.

A bana ma kamar kowacce shekara, duk da Shehin Malamin na daure a hannun gwamnatin tarayya, amma ya yi umurni da 'yan uwansa na jini da wasu ba'adin almajiransa da a baiwa duk wadanda aka san yana baiwa wannan tallafi a lokacin da yake nan a duk Unguwannin Zariya. Kuma tallafin na bana na kayan abincin ya nunka na koyaushe yawa. Kuma tuni aka mika su ga inda ya dace.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, dan uwansa Sayyid Badamasi Yaqoub ne ya jagoranci raba kayan tallafin. An fara rabon tallafin ne tun daga ranar Talatar, 23 ga watan Mayu da ta gabata.

Shaikh Zakzaky ya raba abinci ga mabukata don Ramadana a Zariya (Hotuna)

Kayan abincin da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya ce a rabawa talakawa a Zaria

KU KARANTA: LABARI MAI DADI: An kammala aikin ruwan Zaria

Al'ummar da suka amfana da wannan tallafi sun yi matukar godiya bisa wannan karamcin da Shehin Malamin yake nuna musu duk da kuwa yana daure, har da mamakinsu na ganin yadda bai manta da su ba. Tare da yi masa addu'ar fatan alheri.

Shaikh Zakzaky ya raba abinci ga mabukata don Ramadana a Zariya (Hotuna)

Lokacin da ake raba kayan abincin

A makon da ta gabata ne dai gwamnatin tarayya ta ce bata da niyayr musgunawa El-Zakzaky da ake cigaba da tsarewa a birnin Abuja. Sai dai kuma tana bashi kariya daga barazanar da ke iya tashi sakamakon samun 'yancinsa.

Shaikh Zakzaky ya raba abinci ga mabukata don Ramadana a Zariya (Hotuna)

Ana ci gaba da raba abinci ga mabukata don Ramadana

Shaikh Zakzaky ya raba abinci ga mabukata don Ramadana a Zariya (Hotuna)

Kayayyakin abincin da za a rabawa mabukata

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Iyalan wasu mutanen da aka tsare a ofishin jami'an tsaro ta farar hula yayin da suke bayyana rashin jin dadinsu da ciga da tsare 'yan uwansu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel