LABARI MAI DADI: An kammala aikin ruwan Zaria

LABARI MAI DADI: An kammala aikin ruwan Zaria

- Gwamnatin jihar Kaduna ta yi nasarar kammala aikin ruwan famfo na Zaria

- Dama can babban matsalar dake addabar al'ummar yankin shine rashin ruwan famfo

- Gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya bukaci al’umma da su dunga biyan kudin ruwan famfo domin samun damar ci gaba da samar da ruwa

Kamar yadda aka sani wata babban matsala dake ci ma al’umman yankin Zaria dake jihar Kaduna tuwa a kwarya ita ce matsala ta rashin ruwan famfo.

An kwashe tsawon shekaru da dama gwamnoni na alkawarin kawo karshen wannan matsala dake addabar al’ummar yankin ta hanyar sama masu ruwan famfo amma sai dai abun ya ci tura shiru kake ji.

KU KARANTA KUMA: Yadda aka kusa damfarar ‘Ya ‘Yan Shugaba Buhari

LABARI MAI DADI: An kammala aikin ruwan Zaria

Gwamnatin jihar Kaduna ta kammala aikin ruwan Zaria

Abun farin ciki shine a daidai lokacin da gwamnati mai ci a yanzu ta APC ke cika shekaru biyu a kan kujerar mulki, gwamnatin jihar Kaduna karkashin Mallam Nasir El-Rufai ta cika daya daga cikin gagaruman alkawaran da ta yi wa daukacin mazauna jihar ta hanyar kammala aikin ruwan famfo na Zaria.

NAIJ.com ta ruwaito cewa ukumomi sun bayyana cewa a yanzu matsalar rashin ruwa ta kau a yankin inda ta zama tarihi, koda dai kashi daya na aikin akayi nasarar kammalawa wanda zai ba da ruwa ga mutanen Zaria da kuma na Sabon Gari.

Ana kyautata zaton cewa a nan gaba kadan za’a kammala sauran aikin da ya rage wanda zai bada damar samar da ruwa ga wasu kananan hukumomi na yankin.

Gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya bukaci al’umma da su dunga biyan kudin ruwan famfo domin samun damar ci gaba da samar da ruwa yadda ya kamata.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com, 'yan Najeriya ne ke korafi kan yadda al'amura ke tafiya a kasuwa:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel