Gwamna Ayo Fayose ya kara yin kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

Gwamna Ayo Fayose ya kara yin kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

– Kwanan nan aka kai wani farmaki gidan Mataimakin shugaban majalisar dattawa

– Fayose yayi tir da shiga gidan Sanata Ike Ekweremadu da Jami’ai su ka yi

– Gwamnan yace Gwamnatin Buhari na kokarin ganin bayan ‘Yan adawa

Duk da Shugaban kasa Buhari ba ya nan bai hana Gwamna Fayose caccakar sa ba.

A cewar sa Gwamnatin Buhari na nema ta murkushe Inyamurai.

Gwamna Fayose yace wannan lokaci mai wucewa ne.

Gwamna Ayo Fayose ya kara yin kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

Fayose ya kara yin kaca-kaca da Buhari

A cewar Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose Gwamnatin Shugaba Buhari na kokarin ganin bayan Inyamurai da ‘Yan adawa don haka ne ma Jami’an tsaro su ka kutsa gidan masaukin baki na Mataimakin shugaban majalisar dattawa.

KU KARANTA: Malamai sun shiga yajin aiki a Nasarawa

Gwamna Ayo Fayose ya kara yin kaca-kaca da Gwamnatin Buhari

Buhari na kokari ya razana ‘Yan adawa-Inji Fayose

Gwamna Fayose yace Buhari na kokarin murkushe Inyamuran da ke Gwamnati irin su Sanata Ike Ekweremadu da ma Nnamdi Kanu jagora tafiyar Biyafara. Sai dai Gwamnan yace duk kama-karyar nan ba za ta daure ba.

Can kwanakin baya Sanata Ike Ekweremadu Mataimakin yayi tir da mulkin APC na shugaba Muhammadu Buhari. Ekweremadu yace tattalin arzikin Najeriya ya lalace a karkashin wannan Gwamnati ta shugaba Buhari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Najeriya za ta gyaru kuwa [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel