Duk abin da nayi umarnin Jonathan ne Inji wani tsohon Minista da ke Kotu

Duk abin da nayi umarnin Jonathan ne Inji wani tsohon Minista da ke Kotu

– Ministan shari’a a lokacin shugaba Jonathan ya fadawa Kotu cewa bai da laifi

– Ana shari’ar ne a babban Kotun Tarayya da ke Abuja

– Daga cikin wanda ake zargi akwai shi Ministan da wasu Jami’ai

An dai samu badakala wajen saida rijoyin man kasar na Malabu.

Yanzu haka EFCC ta maka Ministan shari’a a lokacin Jonathan Kotu.

Haka kuma ana karar wani tsohon Ministan mai da wani Dan kasuwa.

Duk abin da nayi umarnin Jonathan ne Inji wani tsohon Minista da ke Kotu

Jonathan ya wawari wasu makudan kudi ta rijiyoyin mai?

Akwai dai badakalar da aka buga wajen saida rijiyar man kasar nan na Malabu. Hukumar EFCC na tuhumar Ministan shari’a a lokacin Shugaba Jonathan watau Mohammed Bello Adoke. Ana tuhumar tsohon Ministan mai na kasar Dan Etete.

KU KARANTA: An nemi a damfari Iyalin Shugaban kasa

Duk abin da nayi umarnin Jonathan ne Inji wani tsohon Minista da ke Kotu

Adoke ya jefa Jonathan cikin matsala

Adoke ya bayyanawa Kotu cewa duk abin da yayi a wancan lokacin shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya sa shi ya kuma amice. Haka kuma ana zargin wani babban Dan kasuwa Aliyu Abubakar da hannu a cikin badakalar.

Kwanaki Wani Dillalin man fetur ya bayyana cewa Jonathan ya tashi da kusan Dala Miliyan $200 daga cikin kasuwancin Dala Biliyan $1.3 da aka yi na rijiyoyin man Malabu na kasar. Sai dai shi Jonathan yace shi fa bai karbi wasu kudi ba

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC sun yi wani tattaki na yaki da barna

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel