Ba raba Najeriya ba ce mafita Inji wani Dattijon Arewa

Ba raba Najeriya ba ce mafita Inji wani Dattijon Arewa

– Farfesa Ango Abdullahi yace ana bukatar Shugabanni na gari

– Dattijon yace abin da ake bukata shi ne shugabannin da za su iya kula da arzikin Jama’a

–Yace inda su Awolowa da Nnamdi Arzikwe su ka yi kokari kenan

Wasu Yanki na kasar su na kira a raba Najeriya.

Tsohon Shugaban Jami’ar A.B.U ta Zariya yana da ja.

Ango Abdullahi yace rabewa daga kasar ba shi ne mafita ba.

Ba raba Najeriya ba ce mafita Inji wani Dattijon Arewa

Ango Abdullahi ya yabi su Obafemi Awolowa

Tsohon Shugaban Jami’ar A.B.U Zariya Farfesa Ango Abdullahi yace ana bukatar samun shugabannin da za su iya tattalin arzikin da Najeriya ke da shi. A cewar sa hakan ba wai raba kasar ko arziki bane zai kawo ga ci.

KU KARANTA: Yadda aka dakatar da binciken Sarkin Kano

Ango Abdullahi yace inda shugabannin baya su Marigayi Obafemi Awolowa da Nnamdi Arzikwe su ka yi kokari kenan wajen tattalin arzikin kasar duk da bai da yawa a wancan lokaci. Ango yayi wannan magana ne lokacin taya Edwin Clark cika shekaru 90.

Kwanaki kun ji cewa Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Balarabe Musa yace dole Inyamurai su nemi a raba Najeriya. Yake cewa an maida su saniyar ware a Najeriya, don haka ne dai su ke kira a raba Najeriya su samu kasar su.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jama'a za su goyi bayan mulkin Soja kuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata

Sarkin Kano ya koka kan rikicin ma’aurata musamman akan mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel