AZUMIN RAMADAN: Gwamnan Bauchi ya raba kayan abinci ga marayu da marasa galihu (HOTUNA)

AZUMIN RAMADAN: Gwamnan Bauchi ya raba kayan abinci ga marayu da marasa galihu (HOTUNA)

- Gwamnan Bauchi ya rarraba kayan abinci ga marayu da marasa galihu

- Ya yi hakan ne domin ganin gwamnatinsa ta faranta wa al’ummar jihar dake karkashin sa

A kokarin sa na ganin gwamnatinsa ta farantawa al'ummar jihar Bauchi, gwamnan jihar Barista M.A Abubakar ya yi wa marayu da marasa karfi goma ta arziki.

Inda aka rarraba masu buhunan kayan masurufi da suka hada shinkafa, dawa, siga, samobita da kayan sawa ga dubban marayu da marasa karfi da suka fito daga kananan hukumomi guda tara dake fadin jihar.

KU KARANTA KUMA: Yadda aka kusa damfarar ‘Ya ‘Yan Shugaba Buhari

AZUMIN RAMADAN: Gwamnan Bauchi ya raba kayan abinci ga marayu da marasa galihu

Gwamnan Bauchi ya raba kayan abinci ga marayu da marasa galihu domin azumin Ramadan

NAIJ.com ta samu labarin cewa wannan shine zagaye na farko na shirin rabon kayan masarufin.

Shirin rabon kayan wanda aka gudanar a karkashin hukumar kula da harkokin marayu da marasa karfi na jihar, an yi hakan ne domin saukaka musu rayuwa a yayin azumin watan Ramadan.

KU KARANTA KUMA: Ana cacar baki tsakanin Jonathan da El-Rufai

Kananan hukumomin da suka amfana da kayan sun hada da Katagum, Misau, Gamawa, Shira, Giade, Dass, Tafawa Balewa, Dambam da Toro. Dukkan mazabun dake kananan hukumomin za su amfana da shirin.

AZUMIN RAMADAN: Gwamnan Bauchi ya raba kayan abinci ga marayu da marasa galihu

Kayayyakin sawa da aka rarraba wa jama'a

AZUMIN RAMADAN: Gwamnan Bauchi ya raba kayan abinci ga marayu da marasa galihu

Kayan abinci da aka rarraba wa marayu da marasa galihu

AZUMIN RAMADAN: Gwamnan Bauchi ya raba kayan abinci ga marayu da marasa galihu

Gwamnan Bauchi ya raba kayan abinci ga marayu da marasa galihu

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel