Bayan tafiyar Buhari: Osinbajo yayi sababbin nade-nade

Bayan tafiyar Buhari: Osinbajo yayi sababbin nade-nade

– Yayin da Shugaba Buhari ke Landan inda yake jinya

– Mukaddashin Shugaban kasa ya amince da wasu sababbin nadi

– A ciki har da Shugaban Hukumar fansho na kasa

Farfesa Osinbajo ya nada wasu mukama har 9 a jiya

Doherty zai maye gurbin Anohu da Shugaba Buhari ya sallama

Sai Majalisa ta tantance sa kafin ya soma aiki

Bayan tafiyar Buhari: Osinbajo yayi sababbin nade-nade

Osinbajo yana jan ragamar wani taro

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya nada sabon shugaban Hukumar fansho Funso Dahorty da kuma wasu mutane 8 dabam a jiya. Osinbajo ya kuma nada Ali Usman a matsayin shugaban hukumar kidaya NPC.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ba za ta daga kafa ba wajen yaki da barna

Osinbajo Yemi

Osinbajo ya amince da wasu sababbin nadi

Haka kuma Zaki Magawata, Ben Ovisoun da Nyerere Ayim suna cikin Kwamishinonin Hukumar NPC. Dikko Aliyu ne shugaban Darektocin bankin Masana’antu watau BOI. An kums nada Emeka Nwakpa matsayin shugaban Darektocin Hukumar CPC.

Kwanaki ku ka ji Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo na nema ya karbo bashin Dala Biliyan 1.28 daga bankin Duniya wanda yace an manta ba a rubutawa Majalisa a baya ba. CBN dai na nuna tsoron wajen irin bashin da kasar ke ci.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Osinbajo a wajen taron Biyafara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel