Rundunar sojojin sama ta mallaki karnuka 20 don gane nakiyoyin

Rundunar sojojin sama ta mallaki karnuka 20 don gane nakiyoyin

- Rundunar sojojin sama na Najeriya ta bayyana cewa ta samu karnuka da zasu gane nakiyoyin bam da sauran su

- Sojoji 12 ne aka horar wadanda zasu rike karnukan wajen gano nakiyoyin bam

- A kasar Afirka ta Kudu da kuma cibiyar horaswa na rundunar ‘yan sandan Najeriya aka gudanar da horar

Rundunar sojojin sama na Najeriya ta ce ta samu karnukan tsaro 20 wadanda aka horas da su gane abubuwan fashewa kamar bama-bamai da sauran nakiyoyi don bunkasa yaki da hare-haren ‘yan ta’adda.

Darektan hulda da jama'a da kuma bayanai na sojojin saman Najeriya , Olatokunbo Adesanya ya tabbatar da wannan labari a ranar Alhamis 26 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Hukumar sojin Najeriya ta bayar da agaji ga yara

Adesanya ya ce: “ Sojoji 12 ne a yanzu aka muka horar wadanda zasu rike karnukan kuma ina mai tabbata ceawa karnukan za su taimaka matuka wajen gane nakiyoyin bam da sauran su.”

Rundunar sojojin sama ta mallaki karnuka 20 don gane nakiyoyin

Wannan ne karen da zai iya gane nakiyoyin fasewa

NAIJ.com ta ruwaito cewa an gudanar da horor ne a kasar Afirka ta Kudu da kuma cibiyar horaswa na rundunar ‘yan sandan Najeriya da ke birnin Abuja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku kali fafatawar rundunar sojojin sama da 'yan Boko Haram

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel