Likitocin kasar Afrika ta kudu sunyi dashin mazakuta, karo na biyu a tarihin duniya

Likitocin kasar Afrika ta kudu sunyi dashin mazakuta, karo na biyu a tarihin duniya

Wasu likitocin kasar Afrika ta kudu na jami’ar Stellenbosch University da asibitin Tygerberg Academic Hospital,sunyi tiyatan dashin mazakuta karo na biyu a tarihin duniya.

A wata jawabin da jami’ ar ta saki, tace wani mutum dan shekara 40 ya rasa mazakutarsa shkaru 17 da suka gabata sanadiyar kaciyar da akayi mas aba dai-dai ba. Bayan gudanar da tiyatan, sunce ya fara samun sauki.

Shugaban sashen asibitin, Andre van der Merwe, yace, yana samun sauki sosai. Babu wata alaman rashin daidaito a jijiyoyin, da alamar yana warkewa.

Likitocin kasar Afrika ta kudu sunyi dashin mazakuta, karo na biyu a tarihin duniya

Likitocin kasar Afrika ta kudu sunyi dashin mazakuta, karo na biyu a tarihin duniya

Sai da aka kwashe sa’o’I 9 da rabi ana gudanar da aikin tiyatan.

Jawabin ta cigaba da cewa ana sa ranya samu cikakken sauki cikin watanni 6 masu zuwa. Dakta Jimmy Volmink, yace wannan babban nasara ne wanda ke nuna karfin ilimin likitancin kasar Afrika ta kudu.

KU KARANTA: Buhari ya gaza - Musa

Zaku tuna cewa Van der Merwe ne ya gudanar da irin wannan aiki na farko ne a duniya a shekaran 2014.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel