Kyamar Musulmai ya janyo an kashe mutane 2 a Amurka

Kyamar Musulmai ya janyo an kashe mutane 2 a Amurka

- 'Yan sanda a birnin Portland na Amurka sun ce an kashe wasu mutane biyu

- An kashe su ne a yayinda suka yi kokarin hana wani mutun cin zarafin wasu mata biyu Musulmai

'Yan sanda a birnin Portland na Amurka sun ce an kashe wasu mutane biyu, yayin da suka yi kokarin hana wani mutun cin zarafin wasu mata biyu Musulmai.

Lamarin ya faru ne ranar Juma'a 26 ga watan Mayu a cikin jirgin kasa.

'Yan sandan sun ce mutumin wanda ya rika furta kalaman cin zarafi ga matan, ya dabawa mazan biyu wuka saboda sun yi yunkurin saka baki cikin al'amarin.

KU KARANTA KUMA: Jami'an tsaro sun hallaka 'yan bindiga 14 a Lagas

Wani fasinja guda a cikin jirgin ya samu rauni, kafin a kama maharin.

Majalisar kyautata mu'amala ta Musulunci a Amurka ta ce dole ne shugaban kasa Trump ya dauki mataki kan yawaitar tsanar Musulunci a Amurka.

Majalisar ta zargi shugaban kasar Donald Trump da rura kyamar Musulmai saboda irin kalamansa da kuma manufofinsa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel