Buhari na fifita Yarbawa, ba abinda yayiwa Arewa - Junaid Muhammed

Buhari na fifita Yarbawa, ba abinda yayiwa Arewa - Junaid Muhammed

Wani tsohon sanata, Dakta Junaid Muhammad, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya dage yanata fifita Yarbawan kudu maso yamma.

Yace shugaban kasa baiyi ko dan hanya a arewa ba, ya bada misalign cewa irin wannan abu ne Gooduck Jonathan yayi yayinda baiyiwa yankinsa komai ba cikin shekaru 6.

Yace shugaba Buhari ya gaza wajen farfado da tattalin arzikin ya kasance yanata sukar gwamnatin Jonathan da ta shude.

Yace Buhari ya samu kasha 60 cikin 100 a yaki da ta’addanci, 50 cikin 100 a yaki da rashawa, yayinda kuma yace an saci kudade da sunan taimakawa wadanda yakin ta’addanci ya shafa.

Buhari na fifita Yarbawa, ba abinda yayiwa Arewa - Junaid Muhammed

Buhari na fifita Yarbawa, ba abinda yayiwa Arewa - Junaid Muhammed

“A yau ,yankin kudu maso yamma ne ke jin dadin shugaba Buhari ta hanyar nade-nade da kuma ayyuka irinsu hanyoyi. Baiyiwa Arewa komai ba.

“Irin wannan abu ya faru da Jonathan inda yayi ayyuka wasu yankuna sabanin kudu maso kudu.

“Na amince da cewa yayi (Buhari) kokari amma akwai sauran aikin da zaiyi domin gamsar da yan Najeriya.

KU KARANTA: Shugaba Muhammadu Buhari ya gaza - Balarabe Musa

“Najeriya na bukatan shugaba mai karfi wanda zai aiwatar da maganansa. Buhari bai da lafiya kuma wannan abu ya shafi kokarinsa.

“Ya yanke da shugabancin jam’iyyarsa APC, kuma yana samun matsaloli da yan majalisa da ma’aikatar shari’a."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel