Jami'an tsaro sun hallaka 'yan bindiga 14 a Lagas

Jami'an tsaro sun hallaka 'yan bindiga 14 a Lagas

- Jami’an tsaro sun hallaka yan bindiga goma sha hudu a jihar Lagas

- An yi nasarar hallaka su ne a lokacin da suka kutsa kai cikin wata makaranta a Igbonla, karamar hukumar Epe dake jihar Lagas

- Sun kuma sace dalibai 6 a lokacin da suka kai hari makarantar a ranar Alhamis

Twagar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojin ruwa a birnin Lagos, sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga 14 daga cikin wadanda suka kutsa kai cikin wata makaranta a Igbonla, Epe da ke birnin na Lagas tare da sace wasu dalibai kanana guda 6, a ranar Alhamis din da ta gabata.

An dai sace yaran ne daga wuraren kwanansu da misalin karfe 6 na safiyar ranar ta Alhamis.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya aikata ma dan matarsa rashin imani (HOTUNA)

Kafin sace yaran dai, sau uku, ‘yan bindigar suna hankoron idda nufinsu, wanda basu cimma nasara ba, sakamakon jami;an da aka girke suna tsaron makarantar.

Daga bisani ne suka huda katangar makaranta ta baya, inda suka yi amfani da shi wajen awon gaba da yaran.

Rahotanni sun ce gamayyar jami’an tsaron na cigaba da dannawa cikin jejin da ‘yan bindigar suka boye yaran domin ceto su, kuma a kokarin haka ne suka samu nasarar hallaka 14 daga ciki tare da kuma raunata wasu da dama.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati

Surukar marigayi Bilyaminu, Maimuna Aliyu tana kotu bisa tuhumar wawurar dukiyar gwamnati
NAIJ.com
Mailfire view pixel