Wani dan Najeriya ya yi ma dan matarsa mugun duka saboda ya siyo masa biredi a maimakon sigari da ya aike sa (HOTUNA)

Wani dan Najeriya ya yi ma dan matarsa mugun duka saboda ya siyo masa biredi a maimakon sigari da ya aike sa (HOTUNA)

An zargi wani mutumin Najeriya da cin zarafin dan matarsa mai shekaru 6 saboda bai siyo masa abun da ya aike sa ba.

An tattaro cewa mutumin da ba’a ambaci sunan sa ba ya yi ma dan matarsa mugun duka saboda yaron ya yi kuskure gurin siyo abun da aka aike shi.

An aiki yaron wanda aka kira da Emmanuel ya siyo wa mijin mahaifiyarsa sigari sai ya manta ya siyo biredi a maimakon haka.

NAIJ.com ta ci karo da labarin yaron ne bayan a yada a wani shafin Instagram mai suna Basic Rights Counsel (BRC).

Wani mutumi ya aikata ma dan matarsa rashin imani (HOTUNA)

Wani mutumi ya aikata ma dan matarsa rashin imani

A cewar hukumar Basic Rights Counsel, bayan sun ji labarin Emmanuel, sun aika tawagar ceto zuwa gidan yaron.

KU KARANTA KUMA: Wata mata ta kona mijinta da amaryarsa saboda bakin kishi a Arewa

A take aka kai yaron wani babban asibiti amman da suka isa asibitin sai aka gano cewa gwiwar hannunsa ta samu matsala.

An mayar da Emmanuel asibitin koyarwa don samun cikakken kulawa.

Allah ya kyauta don kawai yayi kuskure.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel