Ku roka wa Shugaba Buhari lafiya a wurin ubangiji cikin watan nan - Sakon sultan ga yan Najeriya

Ku roka wa Shugaba Buhari lafiya a wurin ubangiji cikin watan nan - Sakon sultan ga yan Najeriya

- Mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci daukacin musulmai yan Najeriya da su yi wa shugaba Buhari addu'ar samun lafiya a cikin wannan watan mai rahama na Ramadan.

- Sarkin yayi wannan kiran ne a jiya juma'a da dare lokacin da yake sanar da ganin watan na Ramadan a fadar sa dake a garin Sokoto.

NAIJ.com ta tsinkayi sarkin yana cewa: "Kamar yadda shari'ar musulunci ta tanadar, a yau ina mai farin cikin sanar maku da cewa gobe (yau) asabar za'a tashi da azumin watan Ramadan."

Mai karatu dai zai sani cewa musulmai a kasashe daban-daban na duniya ciki har da Najeriya sun fara azumin watan Ramadan ranar Asabar bayan an sanar da ganin wata.

Ku roka wa Shugaba Buhari lafiya a wurin ubangiji cikin watan nan - Sakon sultan ga yan Najeriya

Ku roka wa Shugaba Buhari lafiya a wurin ubangiji cikin watan nan - Sakon sultan ga yan Najeriya

A najeriya majalisar kolin kasar kan addinin Musulunci ne ta sanar da ganin watan Ramadan din.

Mai alfarma sarkin Musulmi, wanda shi ne shugaban majalisar, Sultan Sa'ad Abubakar III, shi nne ya bayyana ganin watan a garuruwa daban-daban a Najeriya a wani taron manema labarai da aka gudanar a daren Juma'a.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure

Majalisar dattawa ta bukaci rundunar sojin Najeriya da ta dawo da jami’in da aka kora bisa kuskure
NAIJ.com
Mailfire view pixel