Ikon Allah! Yadda wayar salula ta ceci ran wata a harin bam

Ikon Allah! Yadda wayar salula ta ceci ran wata a harin bam

- An nuna hotunan wata wayar salula wacce ake zaton ta taimaka wajen ceto rayuwar wata mata 'yar yankin Gwynedd, kuma matar da ta sami raunuka masu yawa a lokacin da aka kai harin bom a birnin Manchester.

- Matar mai suna Lisa Bridgett 'yar asalin garin Pwllheli na kasar Wales ce, tana cikin amfani da wayar ne a ranar Litinin, lokacin da bam din ya tashi, kuma wani notin karfe ya buge ta.

Lamarin ya sa ta rasa yatsarta ta tsakiya kuma notin ya fasa wayarta da kuncinta, inda ya makale a cikin hancinta.

Mijinta ya ce yana ganin wayar ce ta karkatar da notin ta kuma rage karfinsa.

NAIJ.com ta samu labarin cewa harin da aka kai a dandalin wasanni na Manchester Arena ya kashe mutum 22 kuma ya raunata wasu 64. An kama mutane takwas a sanadiyyar harin da Salman Abedi ya kai.

Ikon Allah! Yadda wayar salula ta ceci ran wata a harin bam

Ikon Allah! Yadda wayar salula ta ceci ran wata a harin bam

Madam Bridgett waddad ta tafi wajen kallon mawakiyar tare da 'yarta da kuma 'yar kawarta, ta ce ta yi "sa'a ba ta halaka ba", in ji mijinta Steve.

An yi mata tiyata ranar Talata kuma za a sake yin wani tiyatar ranar Alhamis bayan da aka gano ta sami raunuka a wurare daban-daban har da karaya a kafarta da wani katon rauni a cinyarta.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel