Hakar mai a Arewa: Mun gaji da gafara sa, bamu ga kaho ba - Kungiyar ma'ikatan man fetur

Hakar mai a Arewa: Mun gaji da gafara sa, bamu ga kaho ba - Kungiyar ma'ikatan man fetur

Kungiyar Ma'aikatan man fetur ta kasa tayi taronta a Yola jihar Adamawa inda ta kira gwamnati ta gaggauta soma hakan man a arewa maso gabas kada ta bi harsashen cewa mai zai kare ko za'a daina anfani dashi a duniya abun da tace nan da shekaru dubu man fetur zai cigaba da yin tasiri.

NAIJ.com ta samu labarin cewa kungiyar manyan ma'aikatan kanfanoni masu sarrafa man fetur ta Najeriya PENGASAN ta bi sawun kungiyar kasashe masu sarrafa man fetur OPEC wajen kira ga gwamnatin Najeriya ta fadada aikin neman albarkatun man fetur a arewacin kasar tare da bukatar ta sauya tunanin ta na saida matatunta ga 'yan kasuwa.

Hakar mai a Arewa: Mun gaji da gafara sa, bamu ga kaho ba - Kungiyar ma'ikatan man fetur

Hakar mai a Arewa: Mun gaji da gafara sa, bamu ga kaho ba - Kungiyar ma'ikatan man fetur

Masani kan makamashi Dokta Mohammed Ibrahim ya gabatar da bukatar kungiyar a taron kungiyar a Yola fadar jihar Adamawa a cikin wata kasida da ya gabatar yana bayanin kokarin da kasashe da suka ci gaba ke yi na samar da makamashi da zai maye gurbin man fetur da gas don kaucewa gurbatar muhalli da fargabar da ake da ita na karewar man fetur a doron kasa nan da shekaru masu zuwa.

Dokta Ibrahim ya ce bincike ya nuna duniya zata ta ci gaba da anfani da man fetur da gas duk da fargabar da ake da ita kuma ba sai a tekuna kadai ake samun makamashin mai ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel