Buhari ne sanadiyan barin Nnamdi Kanu ya shahara - Omokri

Buhari ne sanadiyan barin Nnamdi Kanu ya shahara - Omokri

- Reno Omokri ya bayyana cewa rufe ma’asasahin Biyafara, Nnamdi Kanu a gidan yari ya kasance babban kuskure a bangaren shugaban kasa Buhari

- Ya ce Nnamdi Kanu ya zamo daya daga cikin mutane mafi shahara a Najeriya saboda matakin Buhari

Reno Omokri, tsohon mataimakin tsohon shugabna kasa Goodluck Jonathan ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da bari Nnamdi Kanu ya shahara.

A cikin wani rubutu da Omokri ya yi a shafin twitter a ranar Juma’a, 26 ga watan Mayu, ya yi ikirarin cewa da’a ce shugaban kasa bai ba da umurnin kama Nnamdi Kanu ba, toh da bai zamo daya daga cikin mutane mafi shahara a Najeriya ba.

“Abu mafi muni da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi shine rufe Nnamdi Kanu a gidan yari. Shine sanadiyan bari ya zamo daya daga cikin shahararrun mutane a Nageriya a yau!”

KU KARANTA KUMA: Dan shekara 18 ya yi wa kanwar shi mai shekaru 8 fyade a Katsina

Buhari ne sanadiyan barin Nnamdi Kanu ya shahara - Omokri

Nnamdi Kanu ya zamo gwarzo bayan ya yi kusan shekaru biyu a kurkuku

Ku tuna cewa a baya NAIJ.com ta rahoto cewa an kama Nnamdi Kanu a ranar 14 ga watan Oktoba, shekarar 2015 a wani masaukin baki dake Lagas.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya ba da umurnin kama Nnamdi Kanu sannan kuma Kanu da aka tsare kusan shekaru biyu ya zamo shaharare a tsakanin masu fafutukan Biyafara a lokacin da yake kulle a gidan yari.

KU KARANTA KUMA: Jami’an yan sanda sun kai farmaki gidan Ike Ekweremadu

A halin yanzu, a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu matasan kungiyar Ohanaeze sun ziyarci Kanu a gidansa sannan kuma sun kaddamar da shi a matsayin sabon shugaban Inyamurai.

NAIJ.com ta samu labarin cewa wadanda suka ziyarce shi sun hada da Mazi Okechukwu Isiguzoro, mataimakin shugaban kungiyar Arthur Obiora, babban sakataren kungiyar Okwu Nnabuike da sauransu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli bidiyon NAIJ.com na lokacin da aka saki Nnamdi Kanu daga kurkukun Kuje:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Gwamna Willie Obiano a Aso Rock (hotuna)
NAIJ.com
Mailfire view pixel