Rundunar sojoji ta kama manyan shugabannin Boko Haram 3 a jihar Niger

Rundunar sojoji ta kama manyan shugabannin Boko Haram 3 a jihar Niger

- An kama shugabannin kungiyar Boko Haram guda uku a jihar Niger

- An kama yan ta’addan ne bayan wani mamaya da rundunar sojin Najeriya ta kai

- An kai mamayan ne a wani matsugunan Boko Haram dake yankin Mokwa dake jihar

- Daya daga cikin yan ta’addan da aka kama ya ce shine ke da alhakin sace marigayi dattijon jihar, Alhaji Shettima Ali Monguno

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kai mamaya a wani matsugunin Boko Haram dake Mokwa a jihar Niger.

A cewar kakakin rundunar sojin Birgediya Janar Sani Usman, mamayar wanda aka kai a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu yayi sanadiyar kamun shugabannin kungiyar ta’adda guda 3.

Kakakin rundunar ya bayyana a wata jawabi a ranar Juma’a, cewa wadanda aka kama sune, Mustapha Muhammed (Adam Bitri), Ali Saleh da kuma Uba Mohammed.

KU KARANTA KUMA: Jami’an yan sanda sun kai farmaki gidan Ike Ekweremadu

Rundunar sojoji ta kama manyan shugabannin Boko Haram 3 a jihar Niger

Rundunar sojoji ta kama manyan shugabannin Boko Haram 3 a jihar Niger

Usman ya bayyana cewa sun kai ga mabuyarsu a kauyen Gidan Mai a hanyar Mokwa-Tegina.

Binciken farko ya tabbatar da cewa daya daga cikin yan ta’addan, Mustapha Muhammed (Adam Bitri) tare da wani Bakura na daga cikin kungiyar yan ta’addan Boko Haram da suka sace marigayi Alhaji Shettima Ali Monguno a Maiduguri a ranar 13 ga watan Mayu na shekarar 2013.

“A yanzu haka ana ci gaba da tambayar yan ta’addan,” cewar Usman.

KU KARANTA KUMA: Dan shekara 18 ya yi wa kanwar shi mai shekaru 8 fyade a Katsina

A halin yanzu, an kashe manoma goma sha daya a kauyen Amarwa dake karamar hukumar Konduga, bayan yan ta’addan Boko Haram sun kai hari kauyen a kokarin sun a neman abinci.

NAIJ.com ta samu labarin cewa kauyen ya kai kimanin kilomita 16 daga Maiduguri sannan kuma yana kusa da Alau Dam wanda ke cike da dakaru amma ba’a samu taimako daga gurin ba a lokacin harin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku bidiyo a kan ra'ayin 'yan Najeriya game da juyin mulki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani

Shugaba Buhari ya zagaye kansa da mahandama - Sanata Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel